An Ruguza Kayayyakin APC a Kaduna, Sojoji Sun kai Dauki

An Ruguza Kayayyakin APC a Kaduna, Sojoji Sun kai Dauki

  • Sojojin Operation Enduring Peace sun shiga tsakani domin hana rikicin siyasa barkewa a Kafanchan da ke Ƙaramar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna
  • Lamarin ya faru ne yayin da wasu magoya bayan jam’iyyar ADC suka kona tsintsiya, alamar jam’iyyar APC, tare da fastocin yakin neman zaɓen jam’iyyar
  • Sojojin sun tarwatsa taron, sun dakatar da kona alamomin jam’iyyun tare da killace yankin domin hana rikicin ƙara ƙamari tsakanin matasan yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Sojojin Operation Enduring Peace (OPEP) sun shiga tsakani domin hana rikicin siyasa a Kafanchan da ke Ƙaramar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Litinin, 5 ga Oktoba, lokacin da sojojin suka amsa kiran neman taimako kan wani rikicin siyasa da ya ɓarke a yankin.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027 ta fara daukar zafi, yan daba sun farmaki tawagar kamfen ADC

Mutane dauke da tutar APC
Yadda ake daga tutar APC a wajen taro. Hoto: All Progressive Congress
Source: UGC

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ne fitar da rahoto kan matakan da sojojin suka dauka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

An kona alamomin APC

Bayan isar sojojin wurin, sun tarar da wasu magoya bayan jam’iyyar ADC suna kona tsintsiya, wadda ita ce alamar jam’iyyar APC, tare da fastocin yakin neman zaɓen APC.

Rahotanni sun ce kona alamomin jam’iyyar na daga cikin abin da aka bayyana a matsayin wata alama ta siyasa, kafin lamarin ya fara ƙara dagulewa.

Sojoji sun shiga tsakani

Majiyoyin tsaro sun ce wata tawagar jami’an tsaro ta Keystone ta riga ta isa wurin, amma yanayin ya ƙara tsananta, lamarin da ya sa sojojin suka shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.

Sojojin sun tarwatsa mutanen da suka taru, tare da dakatar da kona alamomin jam’iyyun siyasa.

Rahoton ya kara da cewa sun kuma killace yankin domin hana ci gaba da rikicin da kuma kare lafiyar jama’a da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin hatsarin jirgi, an shiga sansanin sojojin Najeriya an kashe sama da 10

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An shawo kan lamarin

Bayan shiga tsakani da sojojin suka yi, an samu nasarar shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Jami’an tsaro sun ci gaba da kasancewa a wurin domin tabbatar da cewa ba a sake samun wani rikici ko tashin hankali ba.

Lamarin ya faru ne a lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a Kaduna gabanin zaɓen 2027, inda a baya aka samu arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan ADC a jihar.

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa ’yan bindiga sun shiga Alrahus da ke Millennium City a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, inda maharan suka rika shiga gidaje suna neman mutanen da za su yi garkuwa da su.

Mijin matar mai juna biyu da aka sace ya ce yana Abuja lokacin da matarsa ta kira shi ta sanar da shi cewa wasu mutane na ƙoƙarin tilasta shiga harabar gidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng