'Ka Mun Afuwa': Ɗan Arewa Ya Roƙi Yafiya daga Tinubu bayan Watsi da Tafiyar Atiku

'Ka Mun Afuwa': Ɗan Arewa Ya Roƙi Yafiya daga Tinubu bayan Watsi da Tafiyar Atiku

  • Wani fitaccen amfani da kafafen sada zumunta a Arewa Al’ameen Yabo, ya sauya goyon bayansa daga Atiku Abubakar zuwa Bola Tinubu a 2027
  • Yabo ya nemi afuwar Tinubu kan zaɓen Atiku da ya yi a 2023, yana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da NELFUND sun canza ra’ayinsa
  • Wasu ’yan Najeriya sun goyi bayan matakin Yabo, yayin da wasu suka soki ra’ayinsa, suna danganta gwamnatin Tinubu da tsadar rayuwa da matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta, Al’ameen Yabo, ya sauya ra’ayinsa kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Matashin wanda a baya yake tafiyar Atiku Abubakar ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Matashi ya watsar da tafiyar Atiku bayan gano ayyukan alherin Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun, Atiku Abubakar.
Source: Getty Images

Yabo, wanda aka fi sani da @A__yabo a X, ya wallafa saƙon neman afuwar Tinubu, yana cewa ya yi nadamar zaɓar Atiku Abubakar a 2023.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba

Ya ce cire tallafin man fetur, ƙoƙarin daidaita darajar naira, ƙarancin layukan man fetur da shirin NELFUND sun sauya ra’ayinsa.

Yabo ya kuma ambaci rage matsalolin da suka shafi ASUU a jami’o’i, rage farashin iskar CNG da kuma abin da ya bayyana a matsayin ci gaba wajen yaƙi da rashin tsaro.

Ya ce:

“Mai yiwuwa ba zan yarda da duk abin da gwamnati ke yi ba, amma ba zan iya yin watsi da ci gaban da na yi imanin an samu ba.”

Matashin ya bayyana sauya matsayinsa a matsayin wanda ya kara kwarew kan lamarin siyasa inda ya ce hakan ba yana nufin kasawa ba ne, yana mai cewa:

“Wani lokaci, yarda cewa ka yi kuskure ba rauni ba ne. girma ne. 2023 Atiku ne. 2027 ta BAT ce.”

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya doke Atiku Abubakar na PDP da sauran ’yan takara, kafin ya fara aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki.

Matakin cire tallafin man fetur ya haifar da suka da dama a farkon mulkinsa, musamman saboda hauhawar farashin kayayyaki da ƙarin tsadar rayuwa da ’yan Najeriya suka fuskanta.

Kara karanta wannan

An yi wa jaruma Fati Muhammad rubdugu kan tallata Tinubu

Martanin ’yan Najeriya kan ra'ayin matashin

Saƙon Yabo ya jawo martani iri-iri a X, inda wasu suka nuna goyon baya ga sauya matsayinsa, yayin da wasu suka ƙalubalanci dalilan da ya bayar.

Wasu masu amfani da kafar sun ce sakamakon cire tallafin man fetur, NELFUND da wasu manufofin gwamnati ya sa suka sauya ra’ayinsu, tare da bayyana shirin zaɓen Tinubu a 2027.

Sai dai wasu sun ce sun yi nadamar zaɓar Tinubu a 2023 saboda matsalar tsaro, tsadar rayuwa da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Wani mai sharhi ya ce ya fi ganin Tinubu a matsayin wanda yake da ƙwarewar shugabanci da gudanarwa fiye da Atiku, amma ya shawarci ’yan Najeriya su binciki dukkan ’yan takarar 2027.

Jingir ya ce ba Tinubu yake tallatawa ba

A wani labarin, an ji cewa malamin addinin musuluncin Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa yana da 'yancin ya zabi abin da yake so da abin da ya kwanta masa a rai domin ra'ayinsa ne.

Kara karanta wannan

Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu

Sheikh Jingir ya bayyana cewa ba Shugaba Bola Tinubu yake tallatawa ba, duk da kiran da yake yi na azabi tikitin muslim-muslim.

Kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi amfani da su wajen tallata tikitin muslim-muslim na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.