Kwamishinan 'Yan Sandan Kano Ya Yaba wa Sarki Aminu Ado kan Muhimmin Abin da Ya Yi

Kwamishinan 'Yan Sandan Kano Ya Yaba wa Sarki Aminu Ado kan Muhimmin Abin da Ya Yi

  • SKwamishinan ’yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ya yabawa Aminu Ado Bayero kan bin doka da kuma umarnin jami’an tsaro.
  • Ibrahim Adamu Bakori ya roƙi Sarkin ya dakatar da shirin hawan dawaki zuwa Yakasai domin halartar bikin saukar karatun Alƙur’ani da za a gudanar
  • Sarkin ya ce zaman lafiya da tsaron Kano na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci, tare da yin alkawarin ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Kwamishinan ’yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, saboda girmama doka.

Bakori ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Sarkin ziyarar ban girma a fadarsa da ke Nasarawa, Kano, bayan Sarkin ya sanar da aniyarsa ta yin jerin gwanon hawan dawaki zuwa Yakasai ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun gamu da mumnunan bala'i bayan kai hari a Borno

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ziyarci Aminu Ado
Ibrahim Adamu Bakori da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

’Yan sanda sun roƙi Sarki Aminu Ado

Kwamishinan ya ce manufar ziyararsa ita ce roƙon Sarkin ya dakatar da shirin hawan dokin domin kare zaman lafiya da tsaron jama’a, cewar rahoton jaridar Tribune.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na buƙatar duk wanda ke shirin gudanar da wani taron jama’a na hawan dawaki ko hawa ya gabatar da sanarwar a rubuce aƙalla sa’o’i 72 kafin gudanar da taron.

Sai dai Bakori ya ce a wannan karon jami’an tsaro na roƙon Sarkin da ya soke jerin gwanon gaba ɗaya saboda damuwar tsaro.

An roƙi sarkin ya je taron da mota

Kwamishinan 'yan sandan ya roƙi mai martaba sarkin ya halarci wajen taron da mota, kamar yadda ya saba yi a baya, domin kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar Kano.

Kwamishinan ya bayyana Aminu Bayero a matsayin basaraken gargajiya mai bin doka, wanda a cewarsa ya kasance yana mutunta umarnin jami’an tsaro tare da fifita zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mahaifin dan takarar jam'iyyar ADC

Ya kuma roƙi Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba, da ya ci gaba da mara wa Sarkin baya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masarautar da jami’an tsaro.

Aminu ya yi alkawarin ba jami’an tsaro haɗin kai

A nasa martanin, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gode wa Kwamishinan da tawagarsa bisa ziyarar da suka kai masa.

Sarkin ya tabbatar musu da cikakken haɗin kansa, yana mai cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano na daga cikin abubuwan da ya sa a gaba.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da mara wa duk wani ƙoƙari da ake yi na tabbatar da zaman lafiyar jama’a da kiyaye doka da oda baya.

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yabawa Sarki Aminu Ado
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

'Yan sanda sun gayyaci dan siyasa a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gayyaci wani ɗan siyasa, Hon. Aminu Abdullahi Warkal.

Rundunar 'yan sandan ta gayyace shi ne domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga ba bisa ka’ida ba a wani taron siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng