2027: Alkawarin Sanata Yari bayan Nada Shi Jagoran Yakin Neman Zaben Tinubu
- Sanata Abdulaziz Yari ya amince da jagorantar kwamitin yakin neman zaben APC na 2027 domin tattaro wa Bola Tinubu kari'ar yan Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ne shugaban kwamitin, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima da Nentawe Yilwatda za su taimaka masa
- Sanata Yari ya ce yakin neman zaben zai kasance tattaunawa da al’ummar Najeriya kan makomar kasar gabanin babban zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya amince da nadin da aka yi masa na zama Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2027.
A baya dai, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin yakin neman zaben APC domin shirya gangamin jam’iyyar gabanin zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Janairun 2027, inda ya nada Yari a matsayin Darakta-Janar.

Source: Twitter
A cikin sanarwar da Sanatan ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar 22 ga watan Agusta, 2027, Abdul-Aziz Yari ya fadi yadda zai gudanar da jagorancinsa.
An tsara kwamitin yakin neman zaben Tinubu
Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da tsarin kwamitin.
Shugaba Tinubu zai kasance shugaban kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, zai zama mataimakin shugaban kwamitin.
Haka kuma, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin. Yari zai rike mukamin Darakta-Janar, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance sakataren kwamitin.
2027: Yari ya karbi mukami a kwamitin APC
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 22 ga watan Agusta, Yari ya bayyana jin dadinsa tare da nuna muhimmancin amanar da aka dora masa.

Source: Facebook
Yari ya ce:
“Na amince cikin matukar godiya da cikakken sanin muhimmancinsa. Ina mika godiyata ta gaskiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar bisa amanar da suka dora min, da kuma shugabannin jam’iyyar bisa wannan kwarin gwiwa. Ba zan dauki wannan al’amari da wasa ba.”
Ya bayyana cewa yakin neman zaben ba wai neman kuri’u kadai ba ne, zai kasance tattaunawa da al’ummar Najeriya a kowace jiha, cikin kowane yare da kowace akida, kan makomar da muke ginawa tare.
Wike ya yi magana kan zaben Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana bayan APC ta fitar da kwamitin kamfen shugaban kasa na Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Nyesom Wike ya bayyana cewa wasu tsofaffin daraktocin kamfen sun taimaka wa ‘yan takararsu, amma daga baya suka rasa jihohinsu duk da kokarin da suka rika yi.
Ya ce zai fi mayar da hankali wajen tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a Abuja da jihar Rivers, yana mai cewa sakamako ya fi mukamin kamfen muhimmanci.
Asali: Legit.ng

