APC: 'Dalilin Atiku na Alkawarin Zai Dawo da Tallafin Man Fetur idan an Zaɓe Shi'
- Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi mahana kan ikirarin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce dawo da tallafin zai iya ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati tare da jefa tattalin arzikin ƙasa cikin ƙarin matsaloli
- Ya buƙaci ’yan Najeriya su yi nazari kan manufofin ’yan takarar shugaban ƙasa kafin zaɓen 2027, maimakon yarda da alkawuran da za su ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya soki 'dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar, kan alƙawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Yilwatda ya bayyana matakin na Atiku a matsayin tsananin yunƙurin neman mulki, yana mai cewa hakan na iya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙarin matsaloli.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa a makon jiya ne Atiku, wanda ke neman tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027.
Kalaman Atiku da suka yamutsa APC
Jaridar Punch ta wallafa cewa Atiku, wanda ya yi magana da Hausa yayin wata hira da wata kafar yaɗa labarai ta ADC, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.
“Ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma ina kuɗin? Ina aka kai su? An yi nufin amfani da su wajen rage talauci da taimaka wa yara su je makaranta. Ina kuɗin yanzu? Da alama kawai suna satar su ne."
Wannan magana ta jawo martani daga mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda masu suka suka ce matsayin Atiku ya bambanta da manufofin da ya gabatar gabanin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan
Ba tare da tsoro ba, Kwankwaso ya fadi rukunin mutane 2 da za su gwabza a zaben 2027
A wamcam lokacin da ya ke neman yan Najeriya su zabe shi, an ruwaito cewa ya yi alkawarin cire tallafin man fetur idan ya hau kujerar shugaban kasa.
Yilwatda ya caccaki alkawarin Atiku
Da yake magana ranar Asabar 22 ga watan Agusta, 2026 yayin ziyarar da ya kai hedikwatar ƙungiyar City Boy Movement a Abuja, Yilwatda ya ce ’yan Najeriya sun cancanci samun bayani fiye da alkawuran da ’yan siyasa ke yi a lokacin zaɓe.

Source: Twitter
Ya ce duk wani shiri na dawo da tsarin tallafin man fetur, wanda zai jawo wa gwamnati babban nauyin kuɗi, ya kamata a bincike shi sosai.
Yilwatda ya ce tsawon shekaru uku ana ƙalubalantar jam’iyyun adawa su bayyana abin da za su yi daban idan aka ba su damar mulki, amma har yanzu babu wata cikakkiyar manufa mai ma’ana da gamsarwa da suka gabatar.
Shugaban APC ɗin ya nuna mamaki kan yadda Atiku zai fito da manufar sauya wannan tsari watanni huɗu kacal kafin zaɓen 2027, bayan shafe shekaru uku ba tare da gabatar da cikakken shirin yadda zai tafiyar da gwamnati ba.
Dalilin Atiku ya sauya matsaya kan tallafin fetur
A baya, kun samu labarin cewa Atiku Abubakar ya sauya matsayinsa kan tallafin man fetur, inda ya ce zai dawo da shi idan aka zabe shi shugaban Najeriya a 2027.
Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya kare matakin, yana cewa shugaba mai tausayi ya kamata ya sake duba manufofin da suke jefa jama'a cikin wahala.
Ibe ya ce shirin Atiku zai rage farashin tace man fetur a cikin gida, wanda zai saukaka sufuri, noma, masana'antu da sauran harkokin tattalin arzikin Najeriya.
Asali: Legit.ng

