An Ji Labarin Abin da Shugaban Gwamnonin APC Ya Fada wa Tinubu a Haduwar Farko

An Ji Labarin Abin da Shugaban Gwamnonin APC Ya Fada wa Tinubu a Haduwar Farko

  • Gwamna Hope Uzodimma, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu bayani kan abubuwan da suka faru a kasar yayin da yake hutu
  • Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC (PGF) ya ce suna aiki tukuru domin tabbatar da cewa 'yan kasa sun samu saukin rayuwa
  • Uzodimma ya bayyana cewa sun shirya shiga kamfe gadan-gadan kuma za su yi talla da sauye-sauyen da gwamnati ta kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma ya yi zama da Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya ce ya yi wa Shugaba Bola Tinubu bayani kan abubuwan da suka faru a kasar yayin da shugaban yake hutu a ketare.

Bola Tinubu
Kwanaki da Bola Tinubu ya hadu da Gwamnan Oyo Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haduwar Bola Tinubu da Gwamna Hope Uzodinma

Leadership ta ce Uzodimma ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Tinubu a gidan shugaban kasar da ke Legas ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

2027: Minista ya dage yana yi wa Tinubu aiki domin APC ta yi nasara a jihohi 5

Gwamnan ya ce ganawar tasu ta kasance mai matukar muhimmanci, ya sanar da shugaban kasar halin da ake ciki a Najeriya a yau.

Ya kuma yi masa bayanin ayyukan da Kungiyar gwamnonin APC ta gudanar yayin da yake hutun wata guda a kasashen ketare.

Hope Uzodimma ya ce:

“Shugaban kasa ya dawo daga hutu. Yayin da yake waje, mu kuma muna gudanar da ayyukanmu a Najeriya.
“Saboda haka, ya dace a yi masa bayani kan abubuwan da suka faru a kasar tare da gabatar masa da rahoto kan abubuwan da suke faruwa.”

Aikin da gwamnoni suke yi wa Tinubu

Ya ce ya kuma tattauna da Bola Tinubu kan kokarin da gwamnonin ke yi wajen wayar da kan ’yan Najeriya game da nasarorin gwamnati

Uzodimma ya ce yanzu gwamnonin sun mayar da hankali zuwa tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun fara jin amfanin sauyin da aka kawo.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu

Ya ce gwamnonin ba za su tsaya wajen tallata manufofin Tinubu kawai ba, za su kuma yi kokarin ganin cewa talaka ya ci moriyarsu sosai.

“Manufar sauye-sauyen ta wuce matakin aiwatarwa zuwa tabbatar da cewa al’ummar Najeriya sun samu amfanin sauye-sauyen,”

- Uzodimma

Gwamnonin APC za su fara yakin neman zabe

Da yake magana kan zaɓen 2027, Uzodimma ya ce PGF ta shirya tsaf domin fara ayyukan yakin neman zabe bayan dawowar Tinubu.

Ya ce gwamnonin za su ci gaba da wayar da kan jama’a kan manufofin gwamnatin Tinubu da abubuwan da ta cimma a shekaru uku.

Sanata Uzodimma ya kuma ce gwamnonin za su tabbatar ’yan Najeriya ne za su kasance wadanda za su ci moriyar gyaran da ake yi.

Ya ce hakan zai taimaka wajen ganin al’umma ta fahimci manufofin gwamnati tare da ganin tasirinsu a rayuwarsu na yau da kullum.

Bola Tinubu da Gwamnan Imo
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a ofis da Gwamnan Imo a fadar mulkinsa Hoto: Bayo Onanuga/Hope Uzodinma
Source: Facebook

Minista 1 zai kawo wa Tinubu jihohi 5

Rahoton nan ya ce Dave Umahi ya yi bayanin yadda yake kokarin ganin Bola Tinubu ya ci zabe a Abia, Enugu, Ebonyi, Imo da Anambra.

Kara karanta wannan

Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000

Tun yanzu tsohon gwamnan na Ebonyi yana jin APC za ta ci jihohin Kudu maso gabas saboda ayyuka da mukaman da aka ba su.

Sanata Umahi ya ce Muhammadu Buhari bai yi masu irin abin da Bola Tinubu yake yi ba a lokacin shi kuma yana gwamna a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng