An Tono Tarihi, Rikicin Atiku Ya Jawo Yunkurin Yi wa Shugaban Kasa Juyin Mulki a Najeriya

An Tono Tarihi, Rikicin Atiku Ya Jawo Yunkurin Yi wa Shugaban Kasa Juyin Mulki a Najeriya

  • Donald Duke ya bayyana yadda jita-jitar juyin mulki ta kai ga tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki a lokacin mulkin Obasanjo
  • Ya ce Mbeki ya tambayi gwamnan Neja ko Najeriya na iya fuskantar juyin mulki idan Shugaba Olusegun Obasanjo ya sake lashe zaɓe
  • Duke ya bayyana cewa hakan ta faru ne sakamakon rikicin da ya faru tsakanin Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River, Nigeria - Tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, ya ba da labarin yadda aka fara kishin-kishin din yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo juyin mulki.

Duke, wanda ya jagoranci Cross River daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan a cikin littafin How to Win Elections in Nigeria, wanda Seun Oloketuyi ya rubuta kuma ake shirin fitar da shi nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban jam'iyyar APC ya fadi ya mutu ana tsaka da taron sulhu

Donald Duke
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke Hoto: Donald Duke
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta samu wasu sassa daga littafin, wanda ya yi nazari kan rikice-rikicen siyasar da suka dabaibaye farkon shekarun Jamhuriyar Najeriya ta Hudu.

Duke ya bayyana yadda jita-jitar yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2003 ta kai har fadar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu.

A cikin bayaninsa, Duke ya waiwayi rikicin siyasar da ta dabaibaye ƙoƙarin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na neman wa’adi na biyu, da kuma ƙara tsanantar rashin jituwar da ke tsakaninsa da mataimakinsa, Atiku Abubakar.

Jita-jitar juyin mulki kafin zaben 2023

A cewar Duke, rikicin siyasar ya tsananta matuƙa har ya jawo hankalin jami’an gwamnatin Afirka ta Kudu.

Ya tuna cewa Abdulkadir Kure, wanda a lokacin yake Gwamnan Jihar Neja, ya samu wata waya ba zato daga Bangumzi Sifingo, jakadan Afirka ta Kudu a Najeriya.

Jami’in diflomasiyyar ya shaida wa Abdulkadir cewa Thabo Mbeki, wanda a lokacin shi ne shugaban Afirka ta Kudu, yana son magana da shi.

Kara karanta wannan

Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027

An ruwaito Mbeki ya tambayi Abdulkadir ko gaskiya ne cewa Najeriya za ta iya fuskantar juyin mulkin soja idan Obasanjo ya nemi wa’adi na biyu kuma ya samu nasara.

Tambayar ta ba Abdulkarim Kure mamaki

Ya tambayi Mbeki inda aka samo wannan bayanin. A cewar bayanin Duke, Mbeki ya bayyana tushen bayanin, sai dai Duke bai bayyana sunan wanda ya bayar da bayanin ba a cikin bayaninsa.

Damuwa da abin da ya ji ya sa gwamnan Neja na wancan lokacin ya nufi fadar shugaban ƙasa da ke Abuja domin sanar da Obasanjo abin da ya faru.

A cewar Duke, yadda batun ya kai har kunnen Mbeki ya nuna irin muhimmancin da ake bai wa rikicin siyasar a wajen Najeriya.

Rikicin Atiku da Obasanjo

Lamarin ya faru ne a lokacin da dangantakar Obasanjo da Atiku ta riga ta shiga wani mawuyacin hali. Duke ya tuna cewa Obasanjo ya kira shi da daddare a lokacin rikicin.

Ya ce shugaban ƙasar ya fusata kan abin da yake gani a matsayin cin amanar da mataimakinsa ya yi masa, har ma yana tunanin janye takararsa ta neman wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Nyesom Wike bai zama darakta janar na kamfen Tinubu ba'

Tsohon gwamnan Cross River ya ce ya yi tafiya zuwa Abuja washegari, inda ya yi ƙoƙarin shawo kan Atiku cewa ƙalubalantar shugaban ƙasa mai ci zai kasance wata babbar caca ta siyasa.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar tare da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Domin ƙara bayyana masa abin da yake nufi, Duke ya ce ya zaro taswirar Najeriya ya shimfiɗa ta a kan teburin Atiku.

Daga nan ya tambaye shi ya nuna hanyar samun ƙuri’un da za ta ba shi damar kayar da shugaban ƙasa mai ci wanda ke da cikakken ƙarfin gwamnati a bayansa.

Daga baya Obasanjo ya tsaya takara kuma ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2003, amma dangantakarsa da mataimakinsa ba ta sake komawa yadda take a baya ba.

An gano Sylva ya taimaka a shirin juyin nulki

Kun ji cewa masu bincike sun zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da gudunmuwar kuɗi domin yunkurin juyin mulkin 2025.

Rahotanni sun ce an raba sama da N700m ga jami'an soja, malamai da wasu fararen hula bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262