'A Baya, Ina Goyon bayan Cire Tallafi': Atiku Ya Fadi dalilin Sauya Tunani kan Lamarin

'A Baya, Ina Goyon bayan Cire Tallafi': Atiku Ya Fadi dalilin Sauya Tunani kan Lamarin

  • Atiku Abubakar ya sauya matsayinsa kan tallafin man fetur, inda ya ce zai dawo da shi idan aka zabe shi shugaban Najeriya a 2027
  • Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya kare matakin, yana cewa shugaba mai tausayi ya kamata ya sake duba manufofin da suke jefa jama'a cikin wahala
  • Ibe ya ce shirin Atiku zai rage farashin tace man fetur a cikin gida, wanda zai saukaka sufuri, noma, masana'antu da sauran harkokin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan shirin dawo da tallafin mai a Najeriya.

Atiku ya tabbatar da cewa idan Allah ya ba shi nasara a zaben 2027 zai dawo da tallafin da Bola Tinubi ya cire.

Dalilin da ya sa Atiku ya sauya tunani tare da shirin dawo da tallafin mai
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fadi dalilin sauya tunanin Atiku a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

Atiku ya fadi dalilin shirin dawo da tallafi

Ibe ya ce shugaba ya kamata ya kasance mai shirya sake duba wata manufa idan aiwatar da ita ya jefa 'yan kasa cikin wahala.

Atiku, wanda yanzu yake wakiltar ADC, a matsayin dan takarar shugaban kasa na 2027, ya ce zai dawo da tallafin man fetur

Ya ce cire tallafin ya kara matsin tattalin arziki ga 'yan Najeriya, ba tare da isasshen tabbacin cewa an yi amfani da kudaden da aka samu ba

Ya kuma tambayi abin da ya faru da kudaden da gwamnati ta samu bayan cire tallafin, musamman ko an kashe su wajen inganta kiwon lafiya

Atiku ya amince cewa a baya ya goyi bayan cire tallafin man fetur, amma ya ce sakamakon manufar ya sa ya sake duba matsayinsa.

Sabon matsayar Atiku ya jawo sabuwar takaddama da fadar shugaban kasa, wadda ta zarge shi da sauya matsayinsa saboda dalilan siyasa.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya rikita Najeriya da maganar maido tallafin man fetur

Atiku ya magantu kan alwashin dawo da tallafi
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Atiku ya yi martani ga fadar shugaban kasa

Da yake mayar da martani, Ibe ya ce bai kamata a soki Atiku ba saboda ya sake tunanin matsayar da ya dauka a 2023 ba

Ibe ya amince cewa Atiku ya goyi bayan cire tallafin a yakin neman zaben 2023, amma ya ce sauya matsaya ba lallai ne ya zama munafurci ba

Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne ko manufar ta inganta rayuwar talakawa, da kuma ko kudaden da aka samu sun amfani jama'a yadda ya kamata

Ibe ya ce ya kamata a duba ko kudaden sun inganta sufuri, kiwon lafiya, ilimi, samar da ayyukan yi da kuma tallafin jin dadin jama'a

Tinubu ya soki Atiku kan shirin dawo da tallafi

Mun ba ku labarin cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta soki Atiku Abubakar kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓe a 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya fito da cikakken tsarin dawo da tallafi don man fetur ya yi araha

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce shirin Atiku yaudara ne da zai iya kawo cikas ga tattalin arziki.

Atiku ya ce bai taɓa adawa da cire tallafin ba, amma ya tambayi yadda aka kashe kuɗin da aka samu bayan cire tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.