Maganar Wike Ka Iya Tabbata, Gefen Atiku, Obi Sun Magantu kan Yiwuwar Hadaka
- Bangaren Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi magana kan shawarar G-100 na gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a 2027
- Duk da haka, sansanonin Atiku da Obi sun amince da buƙatar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa domin ƙalubalantar Bola Tinubu da APC
- NDC ta ce Peter Obi shi ne ɗan takarar da ta fi so idan adawa ta amince da haɗa kai, yayin da Atiku ke nan da burinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sansanonin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Anambra Peter Obi sun yi magana kan hadaka.
Duka bangarorin biyu sun yi watsi da buƙatar gabatar da ɗan takara guda ɗaya a zaben 2027 domin kalubalantar Bola Tinubu.

Source: Facebook
Wata ƙungiyar matsin lamba mai suna G-100 ce ta yi wannan kira, tana neman jam’iyyun adawa su haɗa kai domin kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027, cewar Punch.
Martanin bangaren Atiku da Peter Obi
Majiyoyi sun ce sansanonin Atiku da Obi sun amince da muhimmancin haɗin gwiwar jam’iyyun adawa, amma ba su shirya barin burinsu na neman shugabanci ba.
Wannan matsayi na iya ƙara dagula ƙoƙarin G-100 na samar da haɗin kan adawa, wanda take ganin shi ne hanya mafi dacewa ta kayar da APC.
Kungiyar G-100, wacce Salihu Lukman, ya haɗa, na neman jam’iyyun adawa su yi aiki tare domin kawo sauyi.
Sai dai matsayoyin da suka fito daga sansanonin Atiku da Obi na nuna cewa samun yarjejeniya kan ɗan takara guda na iya zama abu mai wahala.
Da yake magana da manema labarai, babban mataimakin Atiku kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya ce Atiku ya wuce batun shirya taron jam’iyyun adawa.
Ya ce daga ƙarshe, ’yan Najeriya ne za su yanke hukunci bisa manufofin da ’yan takarar shugaban ƙasa za su gabatar musu lokacin zaɓe.
Shaibu ya ce Atiku ya riga ya gabatar da wasu manufofinsa, ciki har da yadda zai tafiyar da batun tallafin man fetur idan aka zaɓe shi.

Source: UGC
Abin da bangaren Peter Obi ya ce
Shi ma sansanin Obi na ganin tsohon gwamnan Anambra yana da ƙwarewa da goyon bayan siyasa da ake buƙata domin ƙalubalantar Tinubu.
NDC ta maraba da shirin G-100 na haɗa kan adawa, amma ta yi watsi da ra’ayin cewa dole ne jam’iyyun adawa su gabatar da ɗan takara guda, cewar Daily Post.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Osa Director, ya ce ya kamata a yaba wa G-100 saboda ƙoƙarin haɗa kan adawa, amma tarihi ya nuna APC ta iya kayar da mai ci.
Ya bayar da misalin zaɓen 2015, inda wasu ɓangarorin jam’iyyun APGA da PDP suka haɗa kai da APC, suka kayar da Shugaba Goodluck Jonathan.
Duk da kin amincewa da ra’ayin ɗan takara guda, ya bayyana cewa NDC ta riga ta yanke shawarar wanda take ganin ya fi dacewa idan aka samu haɗin kai.
Atiku ya fadi kokarinsa game da El-Rufai
Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar yana ganin ba daidai ba ne a zargi jagororin su na jam'iyyar ADC da watsi da Nasir El-Rufai.
‘Dan takaran shugaban kasar ya ce suna yin duk mai yiwuwa saboda tsohon gwamnan na Kaduna ya dawo gida.
Atiku ya ce babu abin da ya hana shi a kama shi face bai aikata wani laifi ba lokacin da yake kan madafun iko.
Asali: Legit.ng


