Ana Wata ga Wata: Babban Kwamandan Hisbah Ya Yi Murabus daga Mukaminsa
- Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr Aminu Usman (Abu Ammar), ya yi murabus daga mukaminsa
- Murabus din ya fara aiki nan take, kamar yadda ya bayyana a wata wasika da ya aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina
- Dr Aminu Usman ya gode wa Gwamna Dikko Umar Radda bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu Ammar, ya yi murabus daga mukaminsa.
Dr Aminu Usman ya sanar da murabus din ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Oktoba, 2026, wadda ya aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

Source: Facebook
Kwamandan Hisbah ya yi murabus
A cikin wasikar da DCL Hausa ta samu kwafi, ya bayyana cewa murabus din nasa ya fara aiki nan take, lamarin da ke nufin ya sauka daga mukamin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar daga ranar da ya mika takardr.

Kara karanta wannan
Dan takarar Sanata ya kwanto kura kan matsalar tsaro, ya nemi Tinubu ya yi murabus
Wasikar murabus ta bayyana godiyar Dr Aminu Usman ga Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima.
Abu Ammar ya gode wa Dikko Radda
Dr Aminu Usman ya nuna godiya ga gwamnan Katsina kan amincewar da ya yi da damar da ya ba shi na jagorantar Hukumar Hisbah ta jihar.
Ya ce ya yi farin cikin kasancewa cikin wadanda suka bayar da gudummawarsu wajen ci gaban Jihar Katsina a lokacin da yake rike da mukamin.
A cewarsa, ya samu damar bayar da gudummawa wajen kokarin inganta zaman lafiya da tsaro a jihar, tare da tallafa wa harkokin kyautata tarbiyyar al’umma.
Murabus din Abu Ammar ya zo ne a lokacin da Hukumar Hisbah ke daga cikin hukumomin da ke taka rawa wajen harkokin da suka shafi kyautata tarbiyya da zaman lafiya a cikin al’umma.

Source: Facebook
Me ysa Abu Ammar ya yi murabus?

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Sai dai a cikin wasikar murabus din da aka ambata, tsohon kwamandan Hisbah bai bayyana wani dalili na musamman da ya sa ya yanke shawarar barin mukaminsa ba.
Haka kuma, bayanan da aka gabatar ba su bayyana wanda zai maye gurbinsa a matsayin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ba.
A karshen wasikar, Dr Aminu Usman ya yi wa Gwamna Dikko Umar Radda addu’ar samun nasara a ayyukansa na jagorantar Jihar Katsina.
Hisbah ta hana wani biki a Yobe
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Hisbah ta dakatar da wani bikin 'Colour Festival' da wasu matasa suka shirya a jihar Yobe, tana mai cewa ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne domin kare tarbiyya, kiyaye ƙa'idodin addinin Musulunci da kuma hana ayyukan da take ganin sun saɓa wa koyarwar addinin Allah.
Hisbah ta kuma yi gargaɗi cewa za ta ɗauki matakin doka kan duk wanda ya shirya ko ya goyi bayan ayyukan da take ganin sun saɓa wa ƙa'idodin Musulunci
Asali: Legit.ng