Majalisar Wakilai Za Ta Binciki NNPCL da INEC kan Zargin Karkatar da N802bn
- Rahoton da ofishin babban mai binciken kudi ya fitar ya sa majalisa za ta binciki aikin NNPCL da hukumar INEC
- Sai dai, zargin da rahoton binciken kuɗi ya gabatar ba yana nufin an tabbatar da aikata laifin karkatar da N802bn
- Hukumomin da abin ya shafa suna da damar bayar da bayani da hujjoji kafin kwamitin majalisar ya yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai zai binciki wasu hukumomi biyu na Gwamnatin tarayya.
Majalisar tarayya za ta yi wa jami’an Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) tambayoyin bincike.

Source: Facebook
Binciken kashe kudin gwamnati ya tado zargi
Rahoton Punch ya ce za a taso jami’an a gaba saboda zargin karya dokokin kasahe kudi da ya wuce sama da Naira biliyan 800.
Zargin ya fito ne daga rahotannin Babban Mai Binciken Kuɗin Gwamnatin Tarayya na shekarun 2021, 2022 da kuma 2023.
Rahotannin sun yi nuni da matsaloli da suka shafi tsarin sayayya, sarrafa kudin shiga, biyan kudi da bin dokokin kudin gwamnati.
Kwamitin yana karkashin dan Majalisar mai wakiltar Ede North/Ede South/Ejigbo/Egbedore a jihar Osun, Hon. Bamidele Salam.
'Yan majalisa za su fara zaman bincike a yau
Za a fara sauraron wasu hukumomi ranar Litinin, 5 ga Oktoba. Za a kuma yi wa NNPCL da INEC tambayoyi a ranar Talata.
Wani ɗan kwamitin ya ce rahoton binciken shekarar 2021 ya yi zargin samun matsalolin kudi da suka kai N514bn a kamfanin NNPCL.
Bayanan da jami'an NNPCL za su yi wa 'yan majalisa shi zai sa a san irin matakin da za a dauka.
Zunuban da ake zargin NNPCL ya aikata
Daga cikin N514bn da ake tambayar NNPCL a kai akwai zargin cire N343.64bn ba bisa ka’ida ba daga kudin sayar da danyen mai.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci
Rahoton ya kuma nuna cewa an yi zargin ware N83.66bn na wasu kudin shiga sannan kamfanin ya cire N82.95bn ba tare da izini ba.
Haka kuma, an gano gibin N3.75bn da ake zargin ya samo asali ne daga sayar da kayayyakin mai a cikin wadannan shekaru uku.
Majalisar ta bukaci NNPCL ya gabatar da takardun da ke tabbatar da wadannan mu'amaloli tare da bada amsoshin tambayoyinsu.
Bayanin da INEC za ta yi wa majalisa
A bangaren hukumar zabe ta INEC kuwa, rahoton binciken shekarar 2022 ya nuna zargin karya dokokin kudi da sun kai N288.19bn.
Tambayoyin sun shafi hanyoyin sayayya, biyan ƴan kwangila da kuma rashin tura wasu kudi da doka ta tanada.
Rahotannin sun shafi abubuwan da suka faru lokacin tsohon Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda yanzu ya bar ofis.
Ɗan Majalisar ya ce akwai tambayoyi kan yadda aka kashe kudi tun daga zaben shekarar 2019.
Rahoton shekarar 2022 ya ce an biya sama da N5.31bn wajen samar da na'urorin tantance masu kada da kuri’a ba tare da izini ba.
Ana zargin kashe kudin ne babu amincewar Hukumar Kula da Sayen Kayayyakin Gwamnati, amma hukumar na da damar kare kanta.

Source: Facebook
'Dan majalisar Kaduna ya yabi Peter Obi
An ji cewa Hon. Bello El-Rufai ya ji kunya da ya jero manyan da suke kiransu game da halin mahaifinsu yake ciki a tsare.
‘Dan majalisar ya yi maganar irin zumuncin da tsohon abokin gabarsu, Peter Obi yake nunawa tun da aka garkame Nasir El-Rufai.
Bayan tsohon gwamnan ya tallata Bola Tinubu wur-jan-jan, a karshe hukumomi sun kama shi saboda zargin aikata wasu laifuffuka.
Asali: Legit.ng

