Ajali Ya Yi Kira: Ango Ya Yi Hadarin Mota Ya Rasu ana Tafiya Daura Masa Aure

Ajali Ya Yi Kira: Ango Ya Yi Hadarin Mota Ya Rasu ana Tafiya Daura Masa Aure

  • Wani matashi mai suna Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Habu, ya rasu a ranar da zai je wajen daurin aurensa a jihar Gombe
  • Abokin mamacin ya ce Habu ya rasu ne sakamakon hatsarin mota, lamarin da ya faru yayin da yake kan hanyar zuwa wajen daurin auren nasa
  • An birne mamacin bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da abokansa da ’yan uwansa suka yi ta addu’ar Allah ya jikansa da rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Wani matashi mai suna Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Habu, ya rasu sakamakon hatsarin mota a ranar da ake shirin daura masa aure a jihar Gombe.

Abokin mamacin, Abubakar Haruna, ne ya sanar da rasuwar mamacin, inda ya bayyana irin alhinin da mutanen da suka san Habu ke ciki.

Kara karanta wannan

Malaman Arewa masu adawa da Tinubu sun bullo, sun yi gagarumin gangami

Abubakar Abdullahi da ya rasu
Angon da ya rasu a kan hanyar zuwa auren shi a Gombe. Hoto: Abubakar Haruna|Babangida Muhammad Gidado
Source: Facebook

Habu ya rasu yana zuwa aurensa

Daya daga cikin abokan shi, Abubakar Haruna ya wallafa a Facebook cewa Habu ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a kan hanyar zuwa wajen daurin aurensa.

Ya ce abin ya zo musu da matukar mamaki, saboda a safiyar ranar har suna tare da mamacin, kafin daga bisani su samu labarin rasuwarsa.

Ya rubuta cewa:

“Cikin alhini da jimami nake sanar da rasuwar abokinmu Abubakar Abdullahi, Malam Habu, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar zuwa daurin aurensa yau. Allahu Akbar, Allah ya jikanka Malam Habu. Da safe nan muna tare, yanzu gashi baya raye.”

An shirya auren a 3 ga Oktoba

Bayanan da ke cikin katin gayyatar da aka wallafa sun nuna cewa an shirya daurin auren Abubakar Abdullahi da Fauziya Abdullahi ne ranar Asabar, 3 ga Oktoba, 2026.

An shirya gudanar da daurin auren ne da ƙarfe 1:00 na rana a Kofar Gidan Alhaji Yahaya Bambam, karamar hukumar Balanga.

Kara karanta wannan

'Ku yi watsi da ɗan siyasar da bai ɗaga wayarku': Sarki ya ba mutane shawara

Sai dai a maimakon a gudanar da bikin da aka shirya, aka koma jana'izar ango bayan rasuwarsa a hatsarin mota.

Abokansa sun yi masa addu'a

Wani abokin Habu, Babangida Muhammad Gidado, shi ma ya bayyana alhininsa kan rasuwar a Facebook, inda ya ce mamacin ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a kan hanyar zuwa daurin aurensa na biyu.

Babangida ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Habu, ya jiƙansa da rahama, sannan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Alhaji Usman Malala da al’ummar Tudun Wada Shamaki da jihar Gombe.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kuma sanar da ’yan uwa da abokan arziki cewa an gudanar da jana’izar mamacin da ƙarfe 5:00 na yamma a Tudun Wada Shamaki, Gombe, a kofar gidan Manu Malala.

Rahotanni sun ce an birne Habu bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da mutane da dama suka yi masa addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama.

Daliba ta ba da mamaki a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Maryam Ummar, wata dalibar Jami'ar Jihar Gombe da ba ta da hannuwa, ta kusa kammala karatun digirinta.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub ya rasu

Maryam ta fuskanci ƙalubale masu yawa a lokacin karatunta, amma hakan bai hana ta ci gaba da neman ilimi ba har ta shiga cikin ɗaliban da za su kammala karatu a jami'ar.

An karrama Maryam saboda jajircewarta, inda wani ya ba ta N50,000, yayin da shugaban jami'ar ya ƙara mata N200,000 domin tallafa mata bayan kammala karatunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng