'Dan Najeriya Ya Ciri Tuta, Ya Zama Shugaban Hukumar WAEC Ta Yammacin Afirka
- Hukumar WAEC ta nada Dr Amos Josiah Dangut daga Najeriya a matsayin sabon shugabanta na Yammacin Afirka gaba dy
- Mista Dangut ya jagoranci reshen hukumar WAEC na Najeriya daga watan Oktoba 2023 zuwa watan Satumba 2026
- Bisa wannana nadi da aka yi masa, sabon shugaban WAEC din zai shafe shekaru biyar daga watan Oktoba 2026 zuwa Satumba 2031
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta nada Dr Amos Josiah Dangut a matsayin sabon shugabanta.
Dangut ya kasance ahugaban reshen hukumar WAEC na Najeriya daga Oktoba 2023 zuwa Satumba 2026.

Source: Facebook
Dan Najeriya ya zama shugaban WAEC
An tabbatar da nadinsa ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Hedikwatar WAEC da ke Accra, Demianus G. Ojijeogu, ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Ranar yanci: Atiku ya ɗauko batun da yan Najeriya ke buƙata sani kan raba tallafin N75,000
Hukumar WAEC ta ce Dangut, wanda dan Najeriya ne, zai yi wa’adin shekaru biyar daga Oktoba 2026 zuwa Satumba 2031, inda ya maye gurbin Alhaji Pateh Bah na Gambia.
Majalisar gudanarwa da je kula da harkokin WAEC ta kasa da kasa, ta amince da nadin nasa a taronta na shekara na 74 da aka gudanar a Accra, Ghana, a watan Maris 2026.
Dangut ya fara aiki a matsayin shugaban hukumar WAEC na 14 a tarihi a ranar 1 ga watan Oktoba, 2026.
Takaitccen tarihin Dangut
An haife shi a ranar 2 ga Oktoba, 1967. Yana da digirin farko a fannin Kiwon Dabbobi da ya samu a 1991, digiri na biyu a fannin Kimiyyar Dabbobi a 1994, da digiti na uku a fannin Kimiyyar Dabbobi a 2017.
Ya fara aikinsa a fannin ilimi a 1994 a St. Louis College, Jos, inda ya yi aiki a matsayin mai tantance jarabawar WAEC kafin ya shiga hukumar a 1998, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya
Kwarewar Dangut a aikin WAEC
Dangut kwararre ne wajen tsarawa da gudanar da jarabawa, kuma ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Mataimakin Shugaban Sashen Tsara Jarabawa da ke Ogba, Legas.
Dangut yana da sama da shekaru 20 na kwarewar aiki kuma an san shi da amfani da Fasahar Sadarwa da Yada Labarai wajen inganta tsara jarabawa, gudanar da ita da kuma ayyukan bayan jarabawa.
A matsayinsa na shugaban WAEC, ya jagoranci wasu muhimman sababbin tsare-tsare, ciki har da fara gudanar da WASSCE ta hanyar kwamfuta, sanya lambobin tantancewa a takardun tambayoyin jarabawa da kuma bullo da tsarin gyara jarabawa ta na'ura.

Source: Facebook
Ya kuma kula da Digital Certificate Portal, WAEC E-Study Platform, Digital Records Archive, da tsarin sarrafa kayan aikin jarabawa da sa ido kan masu tantance jarabawa.
A lokacin aikinsa, kwamitin kula da harkokin jarabawa na Najeriya ya yaba masa kan yadda ya tafiyar da harkokin jarabawa daga 2000 zuwa 2006.
Haka kuma, Gwamnatin Jihar Ondo ta ba shi lambar yabo ta musamman saboda kwazo a lokacin da yake yi wa kasa hidima ta NYSC.
An saki sakamakon WAEC ta 2026
Kun ji cewa hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta 2026, inda sama da ɗalibai miliyan 1.2 suka samu aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Hukumar ta bukaci ɗalibai su mallaki PIN sannan su duba sakamakonsu ta shafukan intanet na WAEC na hukuma.
Asali: Legit.ng
