Trump zai Tsokano Fada da Iran kan Jirgin 'Yan Isra'ila da Ya Samu Matsala a Sama

Trump zai Tsokano Fada da Iran kan Jirgin 'Yan Isra'ila da Ya Samu Matsala a Sama

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa za a kai wa Iran hari mai tsanani idan aka gano cewa tana da hannu a wani lamari da ya shafi jirgin FlyDubai
  • Jirgin FZ1073 da ke kan hanyarsa daga Dubai zuwa Tel Aviv ya sauka ba zato ba tsammani a birnin Tabuk na Saudiyya bayan wani rikici da ya faru a cikin jirgin
  • Trump ya ce Amurka na binciken yiwuwar hannu Iran a lamarin, yayin da FlyDubai ta dakatar da zirga-zirgar jiragenta zuwa kasar Isra’ila har sai baba ta gani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani idan aka tabbatar da cewa tana da hannu a wani lamari da ya shafi jirgin FlyDubai da ke kan hanyarsa daga Dubai zuwa Tel Aviv.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

Trump ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar White House kan ko Amurka za ta dauki matakin ramuwar gayya kan Iran idan aka tabbatar da hannunta a lamarin.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Barazanar Trump ga Iran

NDTV ta wallafa cewa da aka tambaye shi ko Amurka za ta mayar da martani ga Iran idan aka gano tana da hannu a lamarin, Trump ya ce za a kai mata hari mai tsanani.

“Za a kai musu hari mai tsanani, kada ku damu,”

In ji Trump.

Shugaban Amurkan ya ce ya samu wasu bayanai da ke nuna yiwuwar Iran na da hannu a lamarin, amma ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike.

“Zan ce amsar, bisa abin da nake ji, ita ce eh, amma muna aiki kan lamarin a yanzu,”

In ji Trump.

Jirgin FlyDubai ya dura a Sudi

Martanin Trump ya biyo bayan saukar gaggawa da jirgin FlyDubai mai lamba FZ1073 ya yi a birnin Tabuk na Saudiyya.

Turkiye Today ta rahoto cewa jirgin dai ya taso ne daga Dubai zuwa Tel Aviv, amma aka karkatar da shi zuwa Saudiyya bayan wani rikici da ya faru a bangaren matukan jirgin.

Kara karanta wannan

Rikita rikita: Matukan jirgin 'yan Isra'ila sun kaure da fada ana tafiya a sama

Kamfanin FlyDubai ya ce:

“Wani rikici ya faru a dakin matukan jirgin”,

Lamarin da ya sa ma'aikatan jirgin suka shiga domin tabbatar da tsaron jirgin kafin daga bisani aka karkatar da shi zuwa Tabuk.

Mojtaba Khamenei
Shugaban addini na Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daga bisani kamfanin ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Isra’ila da kuma daga Isra’ila, yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

An kai hari Madina

A wani labarin, mun ruwaito cewa kawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya zargi kungiyar Houthi da kai harin jirgi mara matuki kan wata cibiyar raba wutar lantarki a Madina.

Kakakin kawancen, Manjo Janar Turki al-Maliki, ya ce harin ya nufi cibiyar rarraba wutar lantarki ta Taibah da misalin karfe 5:11 na safiyar Talata.

Al-Maliki ya ce binciken da aka gudanar da kuma nazarin tarkacen jirgin mara matukin sun nuna cewa Houthi ce ta shirya tare da kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng