Gwamna Ya ba Malaman Addini Manyan Motoci na Alfarma
- Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bai wa Babban Limamin Ilorin da Majalisar Malaman Ilorin motoci hudu
- Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya yabawa gwamnan bisa cika alƙawari da kuma ci gaba da tallafa wa harkokin addini
- Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, ya ce tallafin zai sauƙaƙa zirga-zirgar malaman addini da ayyukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ilorin, Kwara – Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya miƙa motoci hudu ga Babban Limamin Ilorin da wasu manyan malaman addini a masarautar Ilorin.
An gudanar da bikin miƙa motocin ne a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, inda manyan jami'an gwamnati da shugabannin addini suka halarta.

Source: Facebook
Sanarwar da Mataimakin Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gidan Gwamnatin Kwara, Mashood Abdulrafiu Agboola, ya fitar a Facebook ta ce motocin sun haɗa da sabuwar Toyota Prado ga Babban Limami.
Waɗanda suka amfana da motocin
Baya ga motar Babban Limamin Ilorin, gwamnatin ta kuma bai wa Majalisar Malaman Ilorin motar bas domin sauƙaƙa musu zirga-zirga.
Bugu da kari, Imam Imale, Sheikh Abdullahi AbdulHameed da Imam Gambari, Sheikh AbdulAzeez Sulaiman, sun samu motoci a matsayin tallafi.
Gwamna AbdulRazaq, ta bakin babban mai ba shi shawara Alhaji Saadu Salau, ya ce tallafin na nuna ƙarfafa alaƙar gwamnati da masarautar Ilorin da kuma majalisar malamai.
Sarkin Ilorin ya yabawa gwamna
Da yake karɓar motocin a madadin waɗanda suka amfana, mai martaba sarkin Ilorin ya gode wa gwamna AbdulRazaq bisa cika alƙawarin da ya yi wa Babban Limamin Ilorin.
Sarkin ya ce gwamnatin jihar ta nuna muhimmancin tallafa wa cibiyoyin addini, tare da yi wa gwamnan addu'ar Allah Ya ƙara masa hikima da nasara wajen jagorantar jihar.
A nasa jawabin, Babban Limamin birnin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani ya nuna matuƙar godiya ga gwamnan.
Rahotanni sun nuna cewa ya ce:
"Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, sannan muna matuƙar godiya ga gwamnanmu. Allah Ya ci gaba da kare shi, Ya ba shi kariya daga dukkan sharri."

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa motar bas ɗin da aka bai wa Majalisar Malamai za ta taimaka wajen sauƙaƙa tafiya tare lokacin da suke da taruka ko wasu muhimman ayyuka.
Mutanen da aka sace sun kuɓuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kwara ta sanar da kuɓutar mutanen da aka yi garkuwa da su a hare-haren da aka kai ƙauyukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta bayyana cewa mutanen sun samu 'yanci ne bayan haɗin gwiwar jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Ta kuma yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran jami'an tsaro bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng

