Umahi: Minista Ya Raba Gardama Ya Fadi Abin da Zai Sa Tinubu Ya Zarce a 2027
- Dave Umahi ya ce yana da yakinin Allah zai ba Shugaba Bola Tinubu damar komawa kan mulki a wa’adi na biyu a 2027
- Ministan ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, yana cewa duk da wahalhalun da suka haifar, an ɗauke su ne domin ceto tattalin arziki
- Umahi ya ce Tinubu ya gaji ayyukan tituna 2,068 da darajarsu ta kai kusan N13tn, kuma kusan kashi 80 cikin 100 na ayyukan ma’aikatarsa gadarsu ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya bayyana yakinin cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake samun wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
David Umahi ya ce yana da imanin Allah zai dawo da Shugaba Tinubu kan kujerar shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Umahi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake
Umahi ya danganta tazarcen Tinubu da ikon Allah
Da aka tambaye shi abin da ya sa yake ganin ’yan Najeriya za su iya sake zaɓar Tinubu a 2027, Umahi ya ce yana da cikakken imani da Allah.
“Na yi imani da Allah cewa Allah zai dawo da shi kan mulki,” in ji ministan.
Ya ƙara da cewa Allah ne ke bayar da mulki, kuma Allah ne Ya kawo Tinubu kan mulki, musamman ganin yadda ya karɓi ragamar ƙasa a lokacin da tattalin arziki ke fuskantar matsaloli.
“Ya zo ne a wani lokaci mai matuƙar wahala. An jefa masa nau’o’in ƙalubale daban-daban. Mulki na Allah ne, kuma Allah ne Ya kawo shi,” in ji Umahi.
Ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu
Ministan ya yi watsi da ra’ayin cewa yana yabon shugaban ne kawai saboda Tinubu ne maigidansa, yana mai cewa shugaban yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Umahi ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun jawo wa ’yan Najeriya wahala, musamman masu ƙaramin ƙarfi, amma ya ce matakan sun zama dole domin magance matsalolin tattalin arzikin ƙasar.
Da aka tambaye shi kan korafe-korafen ’yan Najeriya da ke fama da matsalar samun abinci, tare da cewa har yanzu ba su ga amfanin sauye-sauyen ba, ministan ya ce ya kamata a auna gwamnatin ne bisa halin tattalin arzikin da ta gada.
Umahi ya ce a kwatanta tattalin arzikin da aka gada
A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su kwatanta manyan ma’aunai na tattalin arziki a lokacin da Tinubu ya hau mulki da yadda suke a yanzu.
Ya ce shugaban ya ɗauki wasu matakai masu wahala ne saboda abin da ya bayyana a matsayin muradin ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki.

Source: Twitter
Malamai sun yi adawa da tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu malaman addinin Musulunci sun yi gangamin adawa da tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Bayanan da aka samu sun bayyana cewa malamai akalla 1,000 ne suka taru a jihar Kano a ranar Lahadi, 4 ga Oktoban 2026 a wajen taron da aka gudanar.
Asali: Legit.ng
