Isa Ali Ibrahim Pantami ya nada Affan Abuya a cikin Hadimansa

Isa Ali Ibrahim Pantami ya nada Affan Abuya a cikin Hadimansa

Mun samu labari cewa Ministan sadarwan Najeriya Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sake yin wani muhimmin nadi a ofishinsa. Hakan na zuwa ne kusan wata guda da Ministoci su ka shiga ofis.

Dr. Isa Ali Pantami ya zabi Mista Affan Abuya ya zama cikin Masu taimaka masa a ofishin Minista. Affan Abuya zai zama babban Hadimin Ministan tarayyar wajen harkoki na musamman.

Affan Abuya ya yi aiki a hukumar nan ta NITDA wanda Isa Pantami ya baro. Kamar yadda mu ka samu labari, Abuya ya kware a wajen harkar bincike da amfani da kafafen sadarwan zamani.

A Ranar Litinin, 18 ga Watan Satumba, 2019, Ministan ya sanar da wannan nadi, inda Ma’aikatar sadarwan kasar ta fitar da jawabin taya Matashin samun wannan mukami ta shafin ta na Tuwita.

Daga hotunan da @ngrcommtech ta fitar, an ga Affan Abuya ne tare da Mai girma Ministan dauke da takardar aikinsa, da kuma wani hoton su na gaisawa da babban Ministan a kan tuburinsa.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya nada Hadimai 2 da za su taya sa hidima

Mista Abuya ya yi Digirinsa ne a Jami’ar na ta Maiduguri da ke jihar Borno watau UNIMAID, ya kuma kammala karatun a shekarar 2014. Abuya ya kware wajen amfani da manhajojin kyamfuta.

Sabon Hadimin Ministan ya taba yin aiki har a majalisar tarayya na fiye da shekara guda daga 2015 zuwa 2016. Daga baya ya koma hukumar NITDA inda yake aiki tun 2017 kawo yanzu.

Kwanakin baya Ministan ya nada Yusuf Abubakar a matsayin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai a kan kafafen sadarwa na zamani. Shi ma Abubakar Ma’aikaci ne a hukumar NITDA.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel