Zaben 2027: Gwamnan Kebbi Ya Ajiye Mataimakinsa, Ya Dauko Sabon Abokin Takara

Zaben 2027: Gwamnan Kebbi Ya Ajiye Mataimakinsa, Ya Dauko Sabon Abokin Takara

  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya maye gurbin mataimakinsa da sabon wanda zai yi takara da shi a babban zaben 2027 mai zuwa
  • Jam’iyyar APC ta ce an sauke mataimakin gwamnan mai ci, Sanata Umar Tafida, ne bisa shawarar kwararrun lauyoyi kan cancantarsa
  • An bayyana cewa Tafida ya amince da matakin, yayin da gwamnan ya musanta cewa akwai wata rashin jituwa tsakaninsa da mataimakinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zabi tsohon Kwamishinan Kudi na jihar, Alhaji Ibrahim Augie, a matsayin sabon abokin takararsa a zaben gwamna na 2027.

Hakan na nufin an sauke mataimakin gwamnan mai ci, Sanata Umar Tafida, daga matsayin abokin takarar Idris a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

'Ba su da sauran mamora a siyasa': Kwankwaso ya ce ta karewa su Ganduje a Kano

An tsayar da sabon dan takarar mataimakin gwamnan Kebbi
Nasir Idris na jihar Kebbi na APC Hoto: Sarki Yahaya
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sakataren Shirya Ayyukan Jam’iyyar APC na Kasa, Alhaji Suleiman Argungu, ne ya sanar da matakin a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2026 a Birnin Kebbi.

An canja dan takara a Kebbi

Channels TV ta kawo rahoton cewa sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ya ce Alhaji Suleima Argungu ya ce an dauki matakin ne bisa shawarar kwararrun lauyoyi dangane da cancantar mataimakin gwamnan na yanzu.

Argungu ya ce:

“An sauke mataimakin gwamnan na yanzu a matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu a babban zaben 2027 bisa shawarar kwararrun lauyoyi.”

Ya kara da cewa an cimma matsayar ne tare da fahimta da amincewar Tafida, yana mai jaddada cewa babu wata rashin jituwa tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

Argungun zai yi takara a Kebbi

Bayan shawarwari da daukar sabon matakin, Argungu ya sanar da Augie a matsayin sabon abokin takarar Gwamna Idris a zaben gwamna na 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitinmu da Peter Obi a 2027'

Gwaman Kebbi ya ce babu baraka a tsakaninsa da mataimakinsa
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bukaci ‘yan siyasa, mambobin APC da magoya bayan jam’iyyar a fadin jihar da su amince da matakin tare da hada kai domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2027.

Shi ma Gwamna Nasir Idris ya yi watsi da rade-radin cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da Tafida inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da bai wa gwamnatinsa hadin kai da goyon.

Augie ya taba rike mukamin Kwamishinan Kudi na Jihar Kebbi a lokacin mulkin tsohon Gwamna Atiku Bagudu. Ya fito ne daga karamar hukumar Augie ta jihar.

Gwamnan Kebbi ya daui alkawari

A baya, mun kawo labarin cewa wamnan Kebbi, Nasir Idris, ya yi alkawarin tallafa wa iyalan ’yan sanda 10 da ’yan ta’adda suka kashe yayin gudanar da ayyukan tsaro.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da tawagar babban sufeton ’yan sanda, Olatunji Disu, ta kai masa ziyarar ta’aziyya a Birnin Kebbi bayan mummunan harin da ya jawo asara.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Mataimakin babban sufeton ’yan sanda, Umar Dada, ya ce rundunar za ta ƙara ƙoƙari wajen kama waɗanda suka kai harin tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng