Pantami na Murnar Samun Tikitin PDP, Abokin Hamayyarsa Ya Sha Alwashin Jawo Masa Matsala

Pantami na Murnar Samun Tikitin PDP, Abokin Hamayyarsa Ya Sha Alwashin Jawo Masa Matsala

  • Khamisu Ahmed Mailantarki ya ce shi ne ya lashe zaɓen fitar a gwamnan PDP a Gombe, duk da cewa kwamitin zaɓen ya ayyana Isa Pantami a matsayin wanda ya yi nasara
  • Mailantarki ya yi zargin cewa Pantami bai kamata ya shiga zaɓen ba, yana mai dogaro da abin da ya ce shi ne hukuncin Kotun Ƙoli kan cancantarsa
  • Ya ce a shirye yake ya garzaya kotu, har zuwa Kotun Ƙoli, domin neman tabbatar da abin da ya kira nasararsa a zaɓen fitar da gwani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Ɗaya daga cikin masu neman tikitin gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar.

Kara karanta wannan

PDP ta sanar da sakamakon zaben fitar da gwani a Gombe, Pantami ya san makomarsa

PDP ta gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani ranar Talata, 29 ga watan Satumban 2026 wnda kwamitin da Hon. Johnbull Tiemlong Shekarau ya jagoranta ya ayyana Isa Ali Pantami a matsayin wanda ya yi nasara.

Mailantarki ya ce shi ya lashe zabe
Khamisu Mailantarki da Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Hon. Khamisu Mailantarki, Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Mailantarki ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen, Mailantarki ya ce bisa abin da ya kira hukuncin Kotun Ƙoli, bai kamata Pantami ya shiga takarar ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Ya ce kasancewar shi ne ya zo na biyu a zaɓen, kuma bisa fahimtarsa game da hukuncin kotun kan cancantar Pantami, ya kamata a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

“Saboda haka, da yake na zo na biyu a zaɓen, kuma bisa hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya bayyana Pantami a matsayin wanda bai cancanci tsayawa takara ba, na yi amanna cewa ni ne wanda ya lashe wannan zaɓen fitar da gwani da jam’iyyarmu ta gudanar yau,” in ji Mailantarki.

Ya ce Pantami yana APC lokacin tantancewa

Mailantarki ya yi zargin cewa a lokacin da kwamitin tantance ’yan takarar PDP ya amince da masu neman takara don shiga zaɓen fitar da gwani na farko, Pantami yana cikin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; Ana neman hana Pantami shiga sabon fitar da gwani na PDP

A cewarsa, zaɓen da aka gudanar ya kamata ya kasance tsakanin shi da Usman Aliyu Garry, wanda ya zo na uku a jerin sakamakon.

Mailantarki ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen neman abin da ya kira hakkinsa, ko da kuwa hakan zai sa ya garzaya kotu.

Mailantarki ya yi barazanar zuwa kotu

Mailantarki ya ce a shirye yake ya ɗauki matakin shari’a domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar.

“Na shirya zuwa kotu, ko da hakan na nufin zuwa Kotun Ƙoli, domin dawo da nasarata a zaɓen fitar da gwani da aka kammala gudanarwa,” in ji shi.
Mailantarki na son tayar rigima a PDP
Khamisu Mailantarki a wajen zaben fitar da gwani na PDP Hoto: Yusuf Alhassan Gombe
Source: Facebook

An so hana Pantami shiga zaben fitar da gwani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Usman Aliyu Garry, wanda ya ƙalubalanci zaɓen fidda gwani na baya da ya haifar da zaɓen Farfesa Pantami, ya nuna adawa da shigar Pantami cikin sabon zaɓen fitar da gwani gwamnan PDP a Gombe.

Usman Aliyu Garry ya ce ya kamata a takaita sabon zaɓen ga ’yan takarar da suka cancanta bisa tanadin hukuncin kotu, yana mai dagewa cewa bai kamata a bar Pantami ya shiga takarar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng