Fatima El Mansouri: Mace Ta Zama Firayim Minista a karo na 2 a Tarihin Kasashen Afrika
- Fatima Ezzahra El Mansouri ta zama Firaministan Morocco, an ba a nauyin kafa sabuwar gwamnati a kasar
- Sarki Mohammed VI ya tabbatar da naɗin nata ne bayan an gama zaɓen 'yan majalisar dokokin a Morocco
- Hakan ya sa El Mansouri ta zama mace ta biyu a ƙasashen Larabawa da ta taba zama Firaminista a tarihi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Morocco - Sarkin Morocco, Mai martaba Mohammed VI, ya naɗa Fatima Ezzahra El Mansouri a matsayin Firaministar ƙasar.
Bayanai sun tabbatar da cewa shugabar ta zama mace ta farko da ta taɓa riƙe wannan matsayi a tarihin Morocco a Arewacin Afrika.

Source: Getty Images
Fatima Ezzahra El Mansouri ta zama Firaminista
Rahoton da Al Jazeera ta fitar ranar Talata ya ce ta zama mace ta biyu a tarihin ƙasashen Larabawa da ta zama Firaminista.

Kara karanta wannan
Hutu ya kare: Shugaba Tinubu ya bar Faransa, ba zai sauka a Abuja ba idan ya dawo Najeriya
Fadar masarautar Morocco ta sanar da naɗin ta ce an ɗora wa El Mansouri mai shekaru 50 alhakin kafa sabuwar gwamnati.
Mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a ƙasashen Larabawa ita ce Najla Bouden ta Tunisia, wadda ta kasance Firaminista a 2021.
Firaministar ta bayyana hakan da abin tarihi
Baya ga haka, ita El Mansouri ta bayyana naɗin nata a matsayin “abin tarihi kwarai”.
Ta ce:
“A karon farko a tarihin ƙasarmu, mace ce ke ɗaukar nauyin jagorantar gwamnati. Wannan abin alfahari ne ba a gare ni kaɗai ba, har ma ga dukkan matan Morocco.”
Naɗin nata ya zo ne kwanaki huɗu bayan sanar da sakamakon zaɓen 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a makon da ya shuɗe.
Jam'iyyar Authenticity and Modernity Party (PAM), wadda El Mansouri ke wakilta, ce ta samu mafi yawan ƙuri'u a zaben da aka yi.
Jam'iyyar ta lashe kujeru 97 daga cikin 395 da ake da su a Majalisar Wakilai, wadda ita ce ƙaramar majalisar dokokin Morocco.

Kara karanta wannan
Kungiyar musulmai ta gano wuri 1 da Shettima ya yi kuskure a taron Majalisar ɗinkin duniya
Kalubalen kafa sabuwar gwamnati a Morocco
Sai dai PAM ba ta samu isassun kujeru da za ta kafa gwamnati ita kaɗai ba. Tana buƙatar kujeru 198 domin samun cikakken rinjaye.
Babban aikin farko da El Mansouri za ta fuskanta shi ne ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da sauran jam'iyyu domin kafa gwamnati.
PAM ta ce a shirye take ta yi aiki tare da dukkan jam'iyyu na siyasa domin a iya kafa gwamnati.
Sai dai wasu jam'iyyun siyasa, ciki har da Justice and Development Party (PJD), sun ce za su kasance cikin 'yan adawa a Morocco.
Sabuwar gwamnatin za ta kuma yanke shawara kan yadda za a shiry gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta FIFA a shekarar 2030.
Wace ce Fatima Ezzahra El Mansouri
Sabuwar firaministar ya yi karatun dokokin kasuwanci na ƙasashen Anglo-Saxon a Jami'ar New York da ke Amurka da tana budurwa.
Ta fara shiga harkokin mulkin ƙananan hukumomi tun tuni. A shekarar 2009 ta bar tarihi da zamanta magajiyar garin Marrakesh.
Bayan kammala wa'adinta na farko, ta sake komawa shugabancin majalisar ƙaramar hukumar Marrakesh bayan zaɓen 2021.
BBC ta ce ta kuma yi aiki a Majalisar Wakilai, aka sake zaɓenta a matsayin 'yar majalisa fiye da sau ɗaya.
A 2021, El Mansouri ta shiga gwamnatin ƙasa, aka naɗa ta Ministar Tsare-tsaren Ƙasa, Bunƙasa Birane, Gidaje da Manufofin Birane.

Source: Getty Images
Ta'aziyyar Najeriya ga Sarkin Morocco
Kwanaki an ji labari an samu mummunar girgizar kasa mai karfin awo 6.8 a kasar Moroko haka aka samu mutane fiye da 600 sun mutu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon jaje da ta’aziyya ga Sarki Mohammed VI na Moroko a sakamakon jarrabawar.
Tinubu ya tabbatar wa kasar Moroko cewa Najeriya tana tare da su wajen farfadowa daga wannan mummuna lamari da ya auka masu.
Asali: Legit.ng
