Yadda Farashin Litar Fetur Za Ta Kasance idan Atiku Ya Dawo da Tallafi

Yadda Farashin Litar Fetur Za Ta Kasance idan Atiku Ya Dawo da Tallafi

  • Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur na iya rage farashin fetur zuwa tsakanin N400 da N500
  • A wata hira da aka yi da shi, Melaye ya ce rage farashin fetur zai kuma taimaka wajen rage tsadar sufuri da kayayyaki a Najeriya
  • Jigon ADC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan shirin jam’iyyar na mayar da Najeriya kasa mai saukin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Sanata Dino Melaye, ya ce shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur na iya rage farashin fetur zuwa tsakanin N400 da N500.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Hakan na zuwa ne yayin da tattaunawa kan tallafin man fetur ya mamaye fagen siyasar zaben shugaban kasa na 2027.

Sanata Dino Melaye
Jigon ADC, Sanata Dino Melaye a wajen taro. Hoto: Dino Melaye
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Melaye, wanda ke cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira.

Farashin mai zai iya komawa N400

Melaye ya ce manufar ADC ita ce ganin an mayar da Najeriya kasa mai saukin rayuwa ta hanyar dawo da tallafin man fetur.

Ya ce idan aka rage farashin fetur daga matakin da ya kai yanzu, ’yan Najeriya za su iya fara sayen litar fetur kan N400 ko N500.

A cewarsa, hakan zai haifar da raguwar farashin sauran kayayyaki saboda farashin man fetur yana da tasiri kai tsaye kan sufuri da zirga-zirgar kaya.

Karin bayani kan tallafin mai

Melaye ya ce cire tallafin man fetur ya kara tsadar rayuwa, yana mai cewa ’yan Najeriya na fuskantar farashin fetur iri daya ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur

Ya ce babu kasuwar APC ko tashar fetur ta wata jam’iyya, saboda kowa yana zuwa kasuwa daya ne kuma yana sayen fetur a farashin da ake sayarwa.

Ya kuma ce farashin fetur yana shafar sufuri, sannan sufuri yana shafar farashin kayayyaki da sauran harkokin tattalin arziki.

Alkawarin da Atiku ya yi

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, ya sha alwashin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi Shugaban Ƙasa.

Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da rashin bayyana yadda aka yi amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Atiku Abubakar
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Sai dai Tinubu ya yi watsi da shirin Atiku, yana mai cewa shawarar ta nuna rashin fahimta mai tsanani game da tafiyar da gwamnati da tattalin arziki.

Obi zai maido tallafin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya ce gwamnatinsa za ta dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027.

Kara karanta wannan

'Za a yi babban haɗari idan Tinubu ya bari aka yi faretin 1 ga Oktoba,' Ayodele

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da jama’a da aka gudanar a Sokoto domin tallafa wa takararsa da ta Rabiu Kwankwaso.

Ya ce zai fara magance matsalar cin hanci da rashawa kafin dawo da tallafin, yana mai cewa cin hanci da rashawa ne babbar matsalar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng