Iyalaina baki daya sunyi addu’a da azumin kwanaki 40 saboda kudirina na takarar gwamna – Inji wani Sanata

Iyalaina baki daya sunyi addu’a da azumin kwanaki 40 saboda kudirina na takarar gwamna – Inji wani Sanata

Sanata mai wakiltan yankin Osun West, Sanata Nurudeen Ademola Adeleke, ya bayyana cewa ahlin gidansa baki daya suyi addu’a da azumin kwanaki 40 kafin su roki Allah akan kudirinsa na takarar gwamna.

Adeleke ya bayyana hakan a sakatariyar jam’iyyar PDP dake Osogbo, babban birnin jihar Osun lokacin da ya gabatar da wasikarsa na son takarar gwamna ga shugaban PDP na jihar, Honourable Soji Adagunodo.

Da yake jawabi ga dandazon jama’a masoyansa da suka taru Adeleke ya bukaci mutanen Osun da su zabe shi sannan yayi alkawarin ci gaba da kyawawan aikin marigayi dan uwansa, Sanata Isiaka Adetunji Adeleke.

Iyalaina baki daya sunyi addu’a da azumin kwanaki 40 saboda kudirina na takarar gwamna – Inji wani Sanata
Iyalaina baki daya sunyi addu’a da azumin kwanaki 40 saboda kudirina na takarar gwamna – Inji wani Sanata

KU KARANTA KUMA: Abunda Dino Melaye yayi bai kamaci sanata ba – Fani-Kayode Abunda Dino Melaye yayi bai kamaci sanata ba – Fani-Kayode

A bangare daban, Sanata Adeleke yace ya cika alkawaran zaben day a dauka ga mazabarsa. Yace zai ba fannin noma kula na musamman idan ya zamo gwamnan jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng