Gwamnan Kebbi Ya Kirkiro Sabuwar Masarauta, Ya Yi Sababbin Nade Nade

Gwamnan Kebbi Ya Kirkiro Sabuwar Masarauta, Ya Yi Sababbin Nade Nade

  • Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da kafa sabuwar gunduma mai kunshe da yankunan kauyuka takwas a karamar hukumar Dandi
  • Dr. Nasir Idris ya kuma amince da nada sabon mai unguwa a karamar hukumar Augie domin karfafa tsarin mulkin gargajiya da inganta shugabanci a matakin kasa
  • Gwamnan ya kuma nada mutumin da zai jagoranci sabuwar gundumar da aka kafa domin gudanar da harkokin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da kafa sabuwar gunduma mai kunshe da yankunan kauyuka takwas a karamar hukumar Dandi ta jihar.

Gwamnan ya kuma amince da nada sabon mai unguwa a karamar hukumar Augie, a wani mataki na karfafa hukumomin gargajiya da inganta shugabanci a matakin kasa.

Gwamna Nasir Idris ya kafa masarauta a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamna Nasir ya yi nade-nade

Kara karanta wannan

Yadda za a sabunta fadar sarkin Gombe ta zama ta yi zarra a Arewa

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Alhaji Garba Umar Dutsinmari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

A cewar kwamishinan, an kafa sabuwar gundumar Buma ne daga tsohuwar gundumar Dolekaina da ke karamar hukumar Dandi, inda aka nada Alhaji Salisu Hakimi a matsayin shugaban gundumar.

Gundumar Buma ta kunshi yankunan kauyuka takwas da suka hada da Tunga Rafi, Gamana, Tudunsan, Gillare, Bump Town, Goraro, Bukki da Alfarma Kwara.

An nada sabon shugaban kauye

Gwamna Idris ya kuma amince da nada Nasiru Umar Maizabo a matsayin mai unguwar Marafan Garin Haruna da ke gundumar Tiggi a karamar hukumar Augie.

Dutsinmari ya ce an yi nade-naden ne bisa tanadin dokar kananan hukumomin Jihar Kebbi ta shekarar 2008, musamman sashe na 10, karamin sashe na (A) da (B), wadanda suka bai wa gwamnati ikon kafa gundumomi da nada shugabannin gundumomi.

An ba su shawara

Kwamishinan ya bukaci sababbin masu sarautar gargajiyar da aka nada da su tabbatar da bin doka da oda, gaskiya, rikon amana da kuma sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, an gano bindigogi 399 da aka yi shirin kawowa Najeriya

“An yi nadinku ne bisa la’akari da tarihin ayyukanku na baya. Ku kasance da tabbacin cewa gwamna da ma’aikatar za su ba ku cikakken goyon baya da hadin kai.” In ji shi

Ana sa ran wannan mataki zai karfafa hukumomin gargajiya tare da inganta gudanar da mulki a matakin kasa a yankunan da abin ya shafa.

An nada hakimi a jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan jihar Kebbi

Gwamnan Kebbi zai ci gaba da auren gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata na shekara-shekara domin tallafa wa marasa galihu a faɗin jihar.

Gwamna Nasir Idris ya bayyana hakan ne yayin bikin ɗaura auren ma'aurata 300 da aka gudanar a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

Dr Nasir Idris ya ce zai ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa mutane masu ƙaramin ƙarfi suna ci gaba da cin gajiyar wannan shiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng