Gwamnatin Bola Tinubu za Ta Ci Bashin Biliyoyin Daloli a Bankin Duniya

Gwamnatin Bola Tinubu za Ta Ci Bashin Biliyoyin Daloli a Bankin Duniya

  • Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan neman sababbin rance uku da yawansu ya kai dala biliyan 1.5
  • Sababbin rancen za su mayar da hankali kan jure sauyin yanayi, tallafa wa iyalai marasa galihu da kuma bunƙasa ilimin yara ƙanana
  • Wannan na zuwa ne yayin da bashin Najeriya ya kai N166.79tn a ƙarshen watan Yunin 2026, lamarin da ke nuna ƙarin N14.39tn cikin shekara guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta buɗe tattaunawa da Bankin Duniya kan sababbin rance uku da jimillar kuɗinsu ya kai dala biliyan 1.5.

Takardun Bankin Duniya sun nuna cewa kowane daga cikin rancen ukun zai kai dala miliyan 500, kuma za a yi amfani da su wajen ayyukan jure sauyin yanayi, tallafin jama'a da bunƙasa yara ƙanana.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya na yi wa 'yan kasa bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rancen ACReSAL ne na farko

Punch ta wallafa cewa na farko shi ne ƙarin rancen dala miliyan 500 da aka tanada domin shirin ACReSAL.

Bankin Duniya ya sanya ranar 29 ga Oktoba, 2026 a matsayin ranar da ake sa ran kwamitin gudanarwarsa zai duba batun rancen.

Gwamnatin Tarayya ce za ta karɓi bashin, yayin da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya za ta aiwatar da shirin.

Sabon rancen zai ƙara yawan kuɗin ACReSAL daga dala miliyan 700 zuwa dala biliyan 1.2, kuma za a samar da dukkan kuɗin ne ta hannun reshen Bankin Duniya da ke bayar da rance mai rangwame.

ACReSAL na aiki a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, inda yake mayar da hankali kan lalacewar ƙasa, ƙarancin ruwa, barazanar sauyin yanayi da raguwar amfanin gona.

Bankin Duniya ya ce hamada da lalacewar ƙasa sun shafi kimanin kashi 43 cikin 100 na fadin ƙasar Najeriya.

Bashin tallafawa jama'a

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Rancen na biyu shi ne dala miliyan 500 domin shirin tallfin da ya shafi tallafawa iyalai marasa galihu.

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ce za ta karɓi rancen, yayin da Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci za ta aiwatar da shirin.

Bankin Duniya ya sanya ranar 30 ga Oktoba, 2026 domin duba tsarin fasaha na shirin, yayin da aka tanadi ranar 16 ga Maris, 2027 domin amincewa da rancen.

Shirin zai samar da tallafin kuɗi na kai tsaye ga iyalai marasa galihu, tare da sabunta rajistar masu cin gajiyar tallafin da haɗa lambar NIN da tsarin bayanan tallafin jama’a.

Bankin Duniya ya ce shirin zai kuma ƙarfafa tsarin aiwatar da tallafin a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rancen ilimin yara ƙanana

Rancen na uku shi ne dala miliyan 500 domin shirin tallafawa ilimin yara kanana a Najeriya.

Ana sa ran za a duba tsarin fasahar shirin a ranar 30 ga Oktoba, 2026, yayin da aka tanadi ranar 15 ga Maris, 2027 domin amincewa da rancen.

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ce za ta karɓi rancen, yayin da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki za ta aiwatar da shirin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya yi magana kan kara albashin ma'aikatan Najeriya

Shirin zai shafi jihohi 36 da Abuja, inda aka tsara samar da ayyukan kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, ilimin farko, kula da yara, ruwa da tsafta ga yara masu shekaru daga haihuwa zuwa biyar.

Atiku Abubakar ya caccaki Bola Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Atiku ya ce albashin N70,000 ya rage daraja saboda tashin farashin man fetur, abinci, sufuri da gidaje, yana mai cewa ya kamata a yi ƙarin albashin da zai dace da tsadar rayuwa.

Gwamnatin Tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 a watan Yulin 2024 bayan tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Tinubu ya ce za a sake duba albashin bayan shekara uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng