Kwankwaso: 'Babu Mai Iya Girgiza Tikitinmu da Peter Obi a 2027'
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce hadin gwiwarsa da Peter Obi ya samar da tikitin mai karfin gaske wanda ya fi karfin sauran yan siyasa a 2027
- Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin inuwar NDC ya kuma bayyana dalilinsa na fadin cewa sun fi kowa karfe
- Ya ce karfin Obi a Kudancin Najeriya da tasirinsa a Arewa za su taimaka wajen samar da gagarumin hadin kan kasa a zaben shugaban kasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tikitin da ya hada shi da Peter Obi ba shi da abokin hamayya wajen amincewar jama’a da kwarewa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2026 a Abuja, inda ya ce hadin gwiwarsa da Obi zai iya kayar da duk wani dan takara a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kuma ruwaito dan takarar yana mai cewa manufarsu ita ce samar da tikitin da zai hada ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da yankinsu ko addininsu ba.
Kwankwaso ya bayyana karfinsu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa tsohon gwamnan Kano ya ce hadin kan nasu ya tattara goyon bayan Obi a Kudancin Najeriya da kuma tasirin siyasarsa a Arewa.
Ya kara da cewa wannan karfi da kowannensu ke da shi zai samar da babbar kafa ta siyasa da za ta hada al’ummar kasar baki daya.
Ya ce:
“Babu wani mutum ko tikiti da zai iya doke namu wajen amincewar jama’a, kwarewa da kuma, ba shakka, kaunar kasa.”
Kwankwaso ya kara da cewa tikitin nasu ya fi sauran ‘yan takara karfi idan aka yi la’akari da tausayin talakawan Najeriya da ke fama da matsaloli.

Source: Twitter
Ya ce:
“Ko ta fuskar tausaya wa talakawa da ke shan wahala a fadin kasar nan a yau, babu wani dan takara da zai iya yin gogayya da mu.”
Kwankwaso ya koda takararsa da Obi
Kwankwaso ya ce kwarewar da ya samu a zaben 2023 ta taimaka masa wajen fahimtar Obi sosai, lamarin da ya tabbatar masa cewa za su iya yin aiki tare.
A cewar Kwankwaso, Najeriya na bukatar sauyin siyasa saboda karuwar matsalar rashin tsaro, talauci, tabarbarewar ababen more rayuwa da kuma kalubalen da manoma ke fuskanta.
Ya ce cire tallafin man fetur bai kawo ingantuwar rayuwar ‘yan Najeriya ba, yayin da manoma ke ci gaba da fuskantar matsaloli saboda shigowar abinci daga kasashen waje cikin farashi mai sauki.
Kwankwaso ya yi magana kan 'shirin' Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyya, tare da bai wa jam’iyyun adawa damar abubuwan da ke bisa doka.
Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira da a tabbatar da ’yancin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, kotuna da hukumomin tsaro, domin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Kwankwaso, wanda ke takarar mataimakin shugaban kasa a NDC shawarci ’yan Najeriya su guji karɓar kyaututtukan ’yan siyasa yayin zaɓe, su yi amfani da lamirinsu wajen zaɓar shugabannin da suka dace.
Asali: Legit.ng

