An Fara: Matasa Sun Yayyaga Hotunan Tallar Tinubu a Arewacin Najeriya
- Wasu matasa a Jega ta jihar Kebbi sun lalata fastoci da allunan tallan Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Nasir Idris yayin zanga-zangar adawa da APC
- Matasan sun rika ihu da kalmar “ba ma so”, yayin da suke lalata wasu fastoci da allunan tallan jam’iyyar a garin
- APC a Kebbi ta nemi jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a zanga-zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Wasu matasa a yankin Jega da ke Jihar Kebbi sun lalata fastocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris a ƙarshen makon nan.
Matasan sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Source: Facebook
Matasa sun rika ihun “bamaso”
Rahotan jaridar Daily Trust ya ce masu zanga-zangar, waɗanda mafi yawansu matasa ne, suna dawowa daga kallon wasan ƙwallon ƙafa ranar Asabar, 26 ga watan Satumban 2026 lokacin da suka fara ihu da kalmar “bamaso”.
Daga nan ne suka fara yayyaga tare da lalata fastocin APC da aka manna a wurare daban-daban.
An kuma ga matasan suna zagayawa a manyan titunan garin, inda suke jifan wasu fastoci da allunan tallan APC tare da lalata su.
An lalata motocin dillalin motoci
A yayin zanga-zangar, matasan sun kuma lalata tare da fasa gilashin motocin wani dillalin motoci da ke yankin.
Sai dai ba a iya tabbatar da dalilin da ya sa matasan suka gudanar da zanga-zangar ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.
Daga bisani jami’an tsaro sun isa yankin, inda suka tarwatsa matasan da ke zanga-zangar. Bayan haka ne aka samu dawowar zaman lafiya a garin.
APC ta nemi a binciki lamarin
Da yake magana kan lamarin a wani taron manema labarai, Sakataren Yaɗa Labarai na APC a jihar, Isah Assalafi, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda suka aikata barnar.

Kara karanta wannan
Amurka ta gode wa Birtaniya da wasu kasashen musulmi 3 kan goyon bayan yaki da Iran
Assalafi ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki mataki mai ƙarfi kan lamarin.
“Su ɗauki mataki cikin gaggawa, su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a zanga-zangar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bai kamata a kare kowa saboda alaƙarsa da siyasa, matsayinsa ko tasirinsa ba.
APC ta yi kira ga sauran jam’iyyu
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga sauran jam’iyyun siyasa da shugabanninsu a jihar Kebbi da su ɗauki alhakin halayen magoya bayansu.
APC ta buƙaci dukkan jam’iyyun da su jajirce wajen gudanar da harkokin siyasa cikin lumana da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Assalafi ya ce APC za ta ci gaba da goyon bayan duk wani mataki da doka ta amince da shi na kare rayuka, tabbatar da tsaron al’umma da kuma kiyaye damar jama’a ta shiga harkokin dimokuraɗiyya a jihar.

Source: Original
Tinubu na cikin koshin lafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta fito ta bayar da tabbaci kan lafiyar mai girma Bola Ahmed Tinubu.
Fadar ta ce Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya, yana kuma ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yayin da yake hutun shekara-shekara a ƙasar waje.
Asali: Legit.ng
