Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi 17 da Kansiloli 260

Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi 17 da Kansiloli 260

  • Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 a zaben ƙananan hukumomin Enugu na 26 ga Satumba, 2026
  • Hukumar zaben Enugu ta ENSIEC ta ce APC ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 260 na mazabu 260 da ke jihar
  • Shugaban hukumar ENSIEC, Farfesa Christian Ngwu, ya bayyana sakamakon zaben a hedikwatar hukumar da ke Enugu ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 a zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Enugu ranar 26 ga Satumba, 2026.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Enugu (ENSIEC) ce ta bayyana sakamakon zaben bayan kammala tattara sakamako.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @APCNigeria
Source: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa shugaban hukumar, Farfesa Christian Ngwu, ya sanar da sakamakon zaben a hedikwatar hukumar da ke Enugu ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

An sanar da sakamakon zaben ƙananan hukumomin Yobe, APC ta sha kaye a mazaɓu 2

Sunayen sababbin ciyamomin Enugu

Ngwu ya ayyana ‘yan takara 17 na APC a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumominsu.

Sunayen yan takarar APC da suka samu nasara a kananan hukumomin Enugu sun hada da:

1. Ugochukwu Nwanjoku - Karamar hukumar Aninri

2. Okolo Uchenna Joseph - Karamar hukumar Awgu

3. Beloved Dan Anike - Karamar hukumar Enugu ta Gabas

4. Onoh Ibenaku - Karamar hukumar Enugu ta Arewa

5. Caleb Ani - Karamar hukumar Enugu ta Kudu

6. italis Chinedu Ngwu - Karamar hukumar Ezeagu

7. Martin Amadieze - Karamar hukumar Igbo Etiti

8. Chris Onyekachi Simon - Karamar hukumar Igbo Eze ta Arewa

9. Ugo Ferdinand Ukwueze - Karamar hukumar Igbo Eze ta Kudu

10. Ani Brendan Emeka - Karamar hukumar Isi-Uzo.

11. Injiniya Mike Ogbuekwe - Karamar hukumar Nkanu ta Gabas

12. John Ogbodo - Karamar hukumar Nkanu ta Yamma

13. Jude Chinedu Asogwa - Karamar hukumar Nsukka.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Shugabannin APC sun hada kai sun yi wa Wike rubdugu

14. Anyaegbudike Greg - Karamar hukumar Oji River

15. Ezeoha Innocent - Karamar hukumar Udenu

16. Agu Hyginus - Karamar hukumar Udi

17. Eezeukwu Chijioke - Karamar hukumar Uzo-Uwani.

APC ta lashe kujerun kansiloli 260

A cewar shugaban ENSIEC, jam’iyyar APC ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 260 da ke cikin mazabu 260 na siyasa a fadin jihar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Yayin da yake bayyana sakamakon zaben, Ngwu ya yaba wa al’ummar jihar Enugu kan yadda suka shiga cikin zaben, yana mai cewa halartar jama’a ya ba tsarin zaɓen ma’ana.

Ya kuma yaba wa hukumomin tsaro, kungiyoyin fararen hula da kafafen yaɗa labarai kan gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da zaben cikin nasara.

Peter Mbah.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah a fadar gwamnatinsa Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

ENSIEC ta ba ciyamomi takardar shaida

Shugaban ENSIEC ya taya ‘yan takarar da suka yi nasara murna, inda ya bukace su da su ɗauki nasarar da suka samu a matsayin kiran da aka yi musu na yi wa jama’a hidima.

Kara karanta wannan

INEC na da 'yan takara ko jam'iyyar da take goyon baya a zaben 2027? An samu bayanai

Daga bisani, hukumar ta miƙa takardun shaidar cin zabe ga sababbin shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka zaɓa.

Gwamnan Enugu ya nada hadimai 101

Kun ji cewa gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya amince da naɗin sababbin hadimai 101 da za su taimaka masa wajen gudanar da mulki.

Waɗanda gwamna Mbah ya nada sun haɗa da masu ba da shawara na musamman (SAs), manyan mataimaka na musamman (SSAs) da mataimaka na musamman (SAs).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262