Martanin Obi ga Masu Karyata Ikirarinsa na Wa'adi 1 a Mulkin Najeriya

Martanin Obi ga Masu Karyata Ikirarinsa na Wa'adi 1 a Mulkin Najeriya

  • Peter Obi ya kara nanata cewa zai yi wa Najeriya wa’adin mulki ɗaya na shekaru huɗu kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027
  • Ya ce tsawon lokacin da shugaba ya yi kan mulki ba shi ne ma’aunin nasara ba, sai dai hidima mai ma’ana da rikon amana da yadda aka tafiyar da kasa
  • 'Dan takarar shugaban kasar da ya hada kai da Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da bayyana dalilansa na aniyar shekaru hudu da abubuwan da zai mayar da hankali a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – 'Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a 2027, zai yi wa’adin mulki ɗaya na shekaru huɗu ne kawai.

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

Obi wanda ya kara nanata matsayarsa ya ce tsawon lokacin da shugaba ya yi a kan mulki ba shi ne ma’aunin nasarar da ya samu a zamaninsa ba.

Peter Obi ya yi magana kan wa'adin mulki 1 a Najeriya
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a Najeriya Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

Obi ya wallafa a shafin X cewa kawo misalan wasu fitattun shugabannin duniya, ciki har da Abraham Lincoln, John F. Kennedy da Nelson Mandela, yana cewa duk da gajeren lokacin da suka yi a mulki, sun bar tarihi da kyawawan abubuwan tunawa.

Obi ya sake magana kan wa'adi 1

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Obi ya ce tsawon watanni 48, wato wa’adin shekaru huɗu, ya isa shugaba mai shiri da mayar da hankali ya yi gagarumin sauyi a ƙasa.

Ya ce:

“Tsawon lokacin da aka yi a kan mulki ba shi ne ma’aunin nasara ba; abin da ke nuna shugabanci na gari shi ne hidima mai ma’ana da rikon amana, ko da kuwa ta kasance na ɗan lokaci. A wannan yanayi nake sake jaddada alkawarina: zan yi wa’adi ɗaya na shekaru huɗu ne kawai idan aka zaɓe ni shugaban ƙasa. Kuma wannan alkawari ba zai canza ba.”

Kara karanta wannan

ADC: 'Abu 1 da zai hana jam'iyyar su Atiku nasara a zaɓen Osun'

Obi ya ce zai gyara Najeriya a shekaru hudu
Peter Obi yayin jawabinsa a gaban wani taron addini Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa:

“Watanni 48 sun isa ga duk wani shugaba da ya mayar da hankali kuma ya shirya tsaf domin yin gagarumin tasiri. Ba na da niyyar wucewa ko da kwana ɗaya bayan haka. Tarihi ya nuna cewa yayin da wasu shugabannin Afrika ke ƙara tsawaita zamansu a kan mulki, akwai yiwuwar mulki ya ƙara lalata su.”

Abin da Obi zai durfafa

Peter Obi ya ce daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai akwai gyaran tsarin mulki, magance matsalar rashin tsaro ta hanyar amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata.

Haka kuma ta bayar da tabbacin cewa gwamnatin da zai jagoranta idan ya samu dama za ta inganta ilimi da kiwon lafiya, tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da sauya Najeriya zuwa ƙasa mai samar da kayayyaki.

Ya ce za a samu wannan ne ta hanyar bunƙasa noma, fasaha da masana’antu, inda ya ce dukkanin masu ganin ba zai iya hakan a cikin shekara daya ba ba su fahimce shi ba.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: 'Dalilina na ganawa da Atiku Abubakar'

Ana son hada Obi, Atiku da yan adawa

A baya, kun samu labarin cewa G-100 za ta gudanar da taron hadin kan jam’iyyun adawa a Abuja ranar 18 ga watan Agusta, 2026, gabanin zaben 2027 domin a hada karfi waje guda.

Kungiyar ta gana da shugabannin jam’iyyun adawa shida domin tattauna yadda za a samar da hadin kai wanda ake sa ran zai samar da dan takarar shugaban kasa daya da zai fafata da Bola Tinubu.

'Yan G-100 sun ce hadin kan adawa zai bukaci sadaukarwa da sassauci daga shugabannin jam’iyyun na adawa, duk da cewa an gaza cimma irin wannan matsaya a baya wajen hadewar yan adawa wuri guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng