'Osun ba Edo ba ce': Davido Ya Bugi Kirji kan Zaɓe, Ya Ce Kawunsa na kan Gaba

'Osun ba Edo ba ce': Davido Ya Bugi Kirji kan Zaɓe, Ya Ce Kawunsa na kan Gaba

  • Fitaccen Mawaki a Najeriya, Davido ya ce kawunsa, Gwamnan Osun Ademola Adeleke, na kan gaba yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna
  • Mawakin ya zargi APC da shan kaye a mazabar tsohon Gwamnan Osun, Bisi Akande, tare da cewa Adeleke na dab da samun nasara
  • Davido ya bukaci al’ummar Osun su kasance cikin taka-tsantsan, sannan hukumomin tsaro su ci gaba da kasancewa a rumfunan zabe yayin kammala tattara sakamako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi ikirarin cewa shan samun nasara a zabe.

Davido ya kawunsa, Gwamnan Osun Ademola Adeleke, ne ke kan gaba a zaben gwamna na Asabar da aka yi.

Mawaki Davido ya ce suna kan gaba a zaben Osun
Mawaki Davido da kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke. Hoto: Davido.
Source: Instagram

Hakan na cikin wasu sakonni da ya wallafa a kafafen sada zumunta yayin da ake ci gaba da tattara kuri’u a fadin Osun, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Gwamna Adeleke ya fadi yadda zai kifar da APC

Davido ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a mazabar tsohon Gwamnan Osun, Bisi Akande.

Ya ce:

“Lamarinsu ya tarwatse! Baba Akande ya sha kaye a mazabarsa, gwamna Adeleke na dab da samun nasara. Kun ji kunyar APC. Osun ba Edo ba ce."

Mawakin, wanda ya fito fili ya yi yakin neman goyon bayan Adeleke, ya kuma bukaci al’ummar Osun su kasance cikin taka-tsantsan tare da dakile abin da ya bayyana a matsayin shirin tsohon Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola.

“Ina rokon mutanen Osun su kasance cikin taka-tsantsan har tsawon daren nan, su kuma dakile shirye-shiryen Oyetola. Osogbo tamu ce! Imole ti woleeeee."

- Davido

A wani sakon kuma, Davido ya bayyana kwarin gwiwar cewa Adeleke zai lashe zaben, inda ya bukaci hukumomin tsaro su ci gaba da kasancewa a wuraren kada kuri’a.

A halin yanzu, jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, sun fara tantancewa da kirga kuri’u a rumfunan zabe daban-daban a Osun bayan kammala kada kuri’a.

Ya zuwa karfe 5:51 na yammacin Asabar, binciken da wakilin jaridar Vanguard ya yi a shafin INEC na duba sakamakon zabe ya nuna cewa an dora sakamakon rumfunan zabe 1,695 cikin 3,763.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Kananan hukumomi 8 da ka iya tasiri wurin samar da wanda zai ci zaɓen

A baya, an ruwaito cewa manyan ‘yan takara uku a zaben sun bayyana kwarin gwiwar samun nasara yayin da aka shiga matakin tantancewa da tattara sakamakon zabe.

Adeleke, dan takarar Accord Party, ya bayyana kwarin gwiwar samun nasara bayan ya kada kuri’arsa a Sagba Abogunde Ward 2, Unit 9, da ke Ede ta Arewa.

Haka kuma, dan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya kada kuri’arsa a Ward 09, Unit 011, Ikire, da ke Irewole, ya bayyana cewa yana da yakinin lashe zaben.

Sanatan APC ya ba masu zaɓe shawara

Kun ji cewa Sanatan da ke wakiltar Osun ta Gabas, Francis Adenigba Fadahunsi, ya bukaci magoya bayansa su sanya ido sosai kan yadda ake kaɗa ƙuri’u a zaɓen gwamnan jihar Osun.

Ana ci gaba da zaben gwamna a jihar Osun yau Asabar 15 ga watan Agusta, 2026 yayin da aka kammala kada kuri'a a wasu rumfunan zabe.

Sanatan ya ja hankalin jama'a a Osun da wajen jihar bayan ya fito karara ya na neman magoya bayansa su hallaka yan adawa, amma ya gyara zancen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.