Nasarar Atiku Abubakar a Zaben 2027 na Iya Jawo Matsala Mai Girma tsakanin Kudu da Arewa

Nasarar Atiku Abubakar a Zaben 2027 na Iya Jawo Matsala Mai Girma tsakanin Kudu da Arewa

  • Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce nasarar Atiku Abubakar na iya kawo ƙarshen tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu
  • Shehu Sani ya yi kira ga jam’iyyun siyasa su tsayar da ’yan takarar shugaban ƙasa daga Kudu a zaɓen 2027 domin mutunta wannan tsari
  • Ya ce Kundin Tsarin Mulki bai hana Atiku ko wani ɗan Arewa tsayawa takarar shugaban ƙasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi gargadin cewa tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa na iya zama tarihi a zaben 2027.

Shehu Sani ya ce nasarar dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar a zaben 2027 na iya kawo karshen wannan tsari a Najeriya.

Shehu Sani.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani Hoto: Shehu Sani
Source: Getty Images

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV ranar Juma’a, yayin da yake cewa ya kamata jam’iyyun siyasa su tsayar da ’yan takarar shugaban ƙasa daga Kudancin Najeriya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Shehu Sani ya yi gargadi kan rikici

“Idan Atiku ya yi nasara, hakan na nufin ƙarshen tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu a Najeriya, kuma hakan zai haifar da fushi da rashin jin daɗi daga Kudancin Najeriya.
"Ba na tunanin kowa zai so ya jagoranci ƙasa mai cike da ƙiyayya, gaba da rikici. A yanzu haka, tsarin siyasa na fama da rikice-rikice da dama,” in ji shi.
“Ba na tunanin ɗan Arewa da zai karɓi mulki a nan zai zo cikin sauƙi kuma cikin kwanciyar hankali ga mutanen Kudancin Najeriya. Amma idan muka bar Kudu ya yi wa’adinsa na shekaru takwas, zuwa shekarar 2031, ɗan Arewa zai karɓi mulki, kuma ba za a samu ƙalubale daga Kudancin Najeriya ba. Wannan shi ne ra’ayina,” in ji Sani.

Shehu Sani ya kare haƙƙin Atiku

Sai dai Sanata Shehu Sani ya amince cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya bai hana Atiku ko wani ɗan Arewa tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

An yi wa su Kwankwaso alƙawarin ƙuri'u miliyan 10 a zaben shugaban kasa na 2027

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Ya yi kira ga jam’iyyun adawa su tsayar da ’yan takarar daga Kudu, domin a bai wa yankin damar fafatawa a neman shugabancin ƙasa a 2027, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shehu Sani ya kuma yi watsi da hujjar cewa yawan al’ummar wani yanki ko yawan masu zaɓensa ya kamata kai tsaye ya ba yankin damar ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa na tsawon lokaci.

Atiku Abubakar ya lashe zaben gwaji

Kun ji cewa Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun samu kuri’a 80,809, kwatankwacin kashi 73.6, a zaɓen shugaban ƙasa na gwaji da aka yi.

Lauya Abba Hikima, wanda ke jagorantar tafiyar Tinubu Must Go (TMG), ya bayyana sakamakon zaben gwaji da aka gudanar kan 'yan takarar da aka fi so a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Abba Hikima ya ce abin da ya fi ba shi mamaki a zaben shi ne yadda sakamakon ya kasance cikin yanayi mai kama da juna a tsawon lokacin da aka gudanar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262