A cikin Sanatoci 109, Wike Ya Fadi Sanatar da Ba Ta Isa Ta Dawo Majalisar dattawa ba

A cikin Sanatoci 109, Wike Ya Fadi Sanatar da Ba Ta Isa Ta Dawo Majalisar dattawa ba

  • Nyesom Wike, ya ganin al'ummar Abuja za su mara wa Philip Aduda da APC baya a zaben Majalisar dattawa a 2027
  • Hakan ya biyo bayan Sanata Ireti Kingibe ta soki yadda ministan yake cin bashi, ta ce an aro kudi ba da amincewar majalisa ba
  • Ministan Abuja ya karyata zargin, kuma ya ja kunnen Kingibe cewa babu ita babu Majalisar Tarayya daga yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya soki wasu maganganu da suka fito daga bakin Sanata Ireti Kingibe.

Sanatar mai wakiltar birnin Abuja a Majalisar dattawa ta zargi Nyesom Wike da karbo aron kudi ba tare da samun izini ba.

Nyesom Wike
Nyesom Wike wajen duba aiki da Sanata Ireti Kingibe tana jawabi a taro Hoto: Lere Olayinka/Ireti Kingibe
Source: Facebook

Nyesom Wike ya karyata Sanata Ireti Kingibe

The Cable ta ruwaito raddin da Ministan na Abuja ya yi wa Ireti Kingibe game da zargin cin bashi babu amincewar majalisa.

Kara karanta wannan

Kotu ta saki fasfon tsohon ministan da ake tuhuma da takardun bogi ya tafi asibitin waje

Wike ya ce kalaman sanatar sun nuna ba ta fahimci yadda gwamnati ke cin bashi ba, ya ce ba a karbo aro babu yardar majalisa.

"Babu ta yadda za ka je ka karbo bashi ba tare da amincewar majalisar tarayya ba.
"Idan kana so ka karbo bashi, za ka sa shi a kasafin kudi sai ka bayyana adadin bashin da gwamnati za ta karbo cikin kasafin kudin."

- Nyesom Wike

Ya ce kamata ya yi Sanata Kingibe ta maida hankali kan ko an yi amfanin da kudin da aka aro wajen yi wa mutanen Abuja ayyuka.

Sanata Kingibe ta ci taliyar karshe in ji Wike

Bayan nan kuma sai Wike ya sake jaddada adawarsa ga tazarcen ‘yar adawar da ke majalisa.

Sun ta rahoto shi yana mai cewa Kingibe ba za ta maimaita kujerarta ba, yana hasashen cewa za ta sha kasa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC

A cewar tsohon gwamnan na Rivers, mutanen Abuja za su bada kuri’un su ne ga Philip Aduda a zaben ‘yan majalisar dattawa.

"Ban so in yi magana game da ita. Tana tattara kayanta ne. Mutanen Abuja sun yi zabi - Za su goyi bayan shugaba Tinubu da Philip Aduda ne a zaben majalisar dattawa."

- Nyesom Wike

Yayin da APC ta ke sa ran Aduda ya sake zama sanata, an ji cewa majalisa ta ce ministan ya bi doka wajen cin basussukansa.

A matsayin sanata, Wike ya ce Ireti Kingibe ba ta tabuka komai ba, babu abin da za a iya nuna wa a ce ta yi wa mutanen mazabarta.

Sanata
Sanatar Abuja, Ireti Kingibe a Zuma Resort Hotel ana aiki Hoto: Ireti Kingibe
Source: Facebook

Tsohon minista zai fita kasar waje

Ana da labari Uche Nnaji ya samu damar zuwa asibiti a lokacin da yake shari'a da hukumar ICPC a kotu kan batun takardun bogi.

Kotu ta amince tsohon Ministan Kimiyya da Fasahan da yake shari’a da ICPC ya tafi kasashen waje domin neman magani.

Alkalin kotun tarayya Abuja ta kuma daga shari'ar da ake yi da Uche Nnaji sai karshen Oktoban 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng