Ana Hurawa Tinubu Wuta Ya Rage Kudin Litar Man Fetur zuwa N500

Ana Hurawa Tinubu Wuta Ya Rage Kudin Litar Man Fetur zuwa N500

  • Kungiyar NLC da kungiyoyin ma'aikatan gwamnati sun buqaci a rage farashin fetur zuwa N500 a kowace lita sannan a maida mafi karancin albashi zuwa N500,000
  • Ma'aikatan sun ba gwamnatin tarayya wa'adin zuwa Laraba, 30 ga watan Satumba, 2026, domin daukar mataki kan buqatunsu saboda tsananin halin matsin lamba
  • Kungiyoyin sun soki rarraba kayan tallafi irin su shinkafa da garri, inda suka bayyana hakan a matsayin tsarin da ba za ya dore ba kuma baya kaiwa ga mabukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kungiyar kwadago ta NLC da haɗakar ƙungiyoyin ma'aikatan gwamnati ƙarƙashin majalisar JNPSNC sun buƙaci gwamnatin tarayya ta maida mafi ƙarancin albashi N500,000 tare da rage farashin fetur zuwa N500.

A cikin wata wasiƙa da suka aike wa Shugaba Bola Tinubu ta hannun Sakataren JNPSNC na ƙasa, Olowoyo Gbenga, ma'aikatan sun nemi da a hanzarta kafa kwamitin da zai tattauna sabon tsarin albashi.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin Najeriya sun ji wuta, sun tura wasiƙa mai zafi ga Shugaba Tinubu

Gidan mai da shugaba Bola Tinubu
Yadda ake sa fetur a gefen hagu da shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Getty Images|Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Vanguard ta rahoto cewa ƙungiyar NLC ta bayyana waɗannan buƙatu a matsayin abubuwan da suka dace da kuma ƙa'ida la'akari da halin da ake ciki.

Batun rage farashin fetur

Ma'aikatan sun jaddada cewa hanya mafi dorewa ita ce rage farashin fetur zuwa N500 a kowace lita, wanda hakan zai tallafi kowa da kowa a ƙasar.

Punch ta ruwaito cewa ƙungiyoyin sun buƙaci gwamnati ta samar da tsarin "tallafin man fetur" ko wata hanyar da za ta sa samun man ya sauƙaƙa.

Sun kuma ba da shawarar cewa gwamnati za ta iya amfani da ƙarin kuɗin da take samu daga kasuwar ɗanyen mai ta duniya wajen rage wa 'yan ƙasa raɗadi.

Gidan mai a Najeriya
Mutane na shan fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Maganar kungiyar NLC

A cewar Shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero, ya kamata gwamnati ta riƙa sayar da ɗanyen mai da Naira ga kamfanonin tace mai na cikin gida sannan ta faɗaɗa matattarar ajiye mai ta ƙasa domin tabbatar da tsaron makamashi.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Dattawa daga Arewa sun aika sako ga Tinubu bayan fetur ya kai N1500

"Wannan babbar hanya ce da za ta samar da ayyukan yi, ƙimar tattalin arziki gami da magance ƙalubalen tsaro da ke saurin sauyawa,"

In ji sanarwar.

Ya kara da cewa Malamai da sauran ma'aikata na buƙatar a hanzarta ƙaddamar da tsarin ƙarin albashi na gaggawa ga ma'aikatan gwamnatin tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi.

Tsarin tallafin sufuri na CNG

A wani labarin, mun ruwaito cewa yayin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin rage kuɗin sufuri daga ranar 1 ga watan Oktoba, jihohi sun fara ɗaukar tsare-tsare kan shirin amfani da CNG.

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci jihohi da su haɗa kai da ƙungiyoyin sufuri domin faɗaɗa amfani da motocin gas, inda rahotanni suka nuna cewa fiye da motoci 120,000 ne aka sauya

Sai dai, 'yan kasuwa da direbobi a wasu jihohin suna korafi kan ƙarancin cibiyoyin zuba gas ɗin, tsadar sauya tsarin motocin, da kuma dogayen layuka a gidajen mai na CNG..

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng