Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Maka Gwamna Kara a Kotu kan Zaben 2027
- APM da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Seyi Makinde, sun kai Gwamnan Abia Alex Otti kotu kan kuɗin N200m da aka sanya wa masu takarar shugaban ƙasa
- Hukumar ABSAA ta kayyade N200m ga masu takarar shugaban ƙasa, N150m ga gwamnoni, da sauran kuɗaɗe ga ’yan takarar majalisun tarayya da jiha
- Makinde da APM na neman kotu ta soke kuɗin, suna cewa ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 da Dokar Zaɓe ta 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Abia - Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Gwamnan Oyo Seyi Makinde, sun kai Gwamnan Abia Alex Otti kotu.
Makinde da APM sun kai kara kotu kan kuɗin N200m da ake buƙata daga masu takarar shugaban ƙasa domin sanya tallan allunan yaƙin neman zaɓe a jihar.

Kara karanta wannan
Sojoji sun cafke kwamandojin 'yan ta'adda da ke da hannu a kisan babban janar a Katsina

Source: Twitter
An shigar da ƙarar mai lamba HC/214/2026 a Babbar Kotun Jihar Abia da ke Umuahia, rahoton jaridar TheCable ya nuna hakan.
Sauran waɗanda aka maka ƙarar sun haɗa da Antoni-Janar na Abia, Hukumar Kula da Alluna da Tallace-Tallace ta Jihar Abia (ABSAA) da Majalisar Dokokin jihar.
ABSAA ta kayyade kuɗaɗen tallan siyasa
A cewar ƙarar, ABSAA ta kayyade N200m ga masu takarar shugaban ƙasa, yayin da masu neman kujerar gwamna za su biya N150m.
’Yan takarar sanata za su biya N100m, masu neman kujerar Majalisar Wakilai N50m, sannan ’yan takarar Majalisar Dokokin Jiha N20m domin samun izinin sanya allunan yaƙin neman zaɓe a jihar.
Makinde da APM suna ƙalubalantar halaccin waɗannan kuɗaɗe, suna mai cewa sun saɓa wa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da Dokar Zaɓe ta 2026.
Makinde da APM sun nemi kotu ta soke kuɗin
Ta hannun lauyansu, Musibau Adetunbi, SAN, masu ƙarar sun gabatar da tambayoyi shida da suke son kotu ta yanke hukunci a kansu, tare da neman wasu umarni guda takwas.
Daga cikin buƙatunsu akwai neman kotu ta soke dokokin da ABSAA ta kafa dangane da yaƙin neman zaɓe, ciki har da kuɗin N200m da aka sanya wa masu takarar shugaban ƙasa.
Sun kuma nemi kotu ta hana waɗanda ake ƙara, wakilansu ko jami’ansu tilasta biyan kuɗin ko cirewa, ɓatawa, lalatawa ko hana sanya allunan tallan yaƙin neman zaɓensu a Abia, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Sun ce INEC ce ke da ikon tsara yaƙin neman zaɓe
Masu ƙarar sun dogara da wasu tanade-tanade na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da kuma Sashe na 92 da 99 na Dokar Zaɓe ta 2026 wajen neman kotu ta bayyana kuɗin N200m a matsayin mara inganci.
Sun ce Dokar Zaɓe ta hana amfani da hukumomin gwamnati ko hukumomin da ke kula da harkokin zaɓe ta hanyar da za ta fifita ko cutar da wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara.
APM da Makinde sun kuma ce Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe sun bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ikon tsara ƙa’idoji da dokokin da suka shafi yaƙin neman zaɓe na ’yan takara da jam’iyyun siyasa.

Source: Facebook
Sun yi nuni da iyakar kuɗin yaƙin neman zaɓe
Masu ƙarar sun kuma dogara da Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda suka ce ya kayyade iyakar kuɗin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashewa a yaƙin neman zaɓe zuwa N10bn.
Sun ce idan kowace jiha za ta sanya irin wannan babban kuɗi ga masu takarar shugaban ƙasa, hakan na iya sa ya zama da wahala a kiyaye iyakar kuɗin da doka ta kayyade.
Hakazalika, sun kuma bayar da hujjar cewa ko da yake jihohi na da ikon tsara harkokin talla, wannan ikon bai kamata a yi amfani da shi ta hanyar da za ta hana ko ta takaita ’yancin ɗan takarar shugaban ƙasa na gudanar da yaƙin neman zaɓe ba.
Sun ƙara da cewa dokokin jihohi ba za su iya rinjayar dokar tarayya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kafa kan harkokin zaɓe ba.
Makinde ya mika mulki ga mataimakinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da bukatar Gwamna Seyi Makinde na tafiya hutun shekara.
Mataimakin gwamnan jihar, Bayo Lawal, ne zai kula da harkokin mulki da gudanar da ayyukan gwamnati har zuwa lokacin da gwamnan zai dawo bakin aiki.
Asali: Legit.ng


