Shugaban Iran Ya Tafi Amurka, zai Fadawa Duniya Abubuwa da Dama
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya sha alwashin girmama matsayar ƙasarsa yayin da yake shirin zuwa birnin New York domin halartar babban taron UN
- Pezeshkian ya ce zai yi amfani da taron wajen bayyana halin da al’ummar Iran ke ciki da kuma matsayinta kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya
- A bayanin da ya yi wa jama'a, shugaban ya ce Iran za ta ci gaba da kare ƙasarta, al’ummarta da kuma abin da ta yi imani da shi cikin mutunci da ƙarfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce zai kare matsayar ƙasarsa da ƙarfi a tarukan ƙasa da ƙasa yayin da yake tafiya birnin New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Tehran kafin ya tashi zuwa New York a safiyar Talata.

Source: Getty Images
Pezeshkian zai kare Iran
Tasnin News ta wallafa cewa Shugaban ya ce ana gudanar da babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana ne ƙarƙashin taken “amincewa”, amma wasu ƙasashe na yin watsi da ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma haƙƙin ƙasashe.
Ya ce taron zai ba shi damar bayyana wahalhalun da al’ummar Iran ke fuskanta tare da nuna ƙarfin ƙasar.
Pezeshkian ya ƙara da cewa zai gana da ’yan siyasa, masu ruwa da tsaki a harkokin al’adu da kafafen yaɗa labarai domin gabatar da matsayar Iran da abin da ke faruwa a zahiri.
Ya ce:
“Za mu kare matsayarmu da ƙarfi a tarukan ƙasa da ƙasa.”
Maganar Iran kan Gaza
Rahoton Kurdistan24 ya nuna cewa Pezeshkian ya ce za su tattauna abubuwan da ke faruwa a Gaza, Falasɗinu, Syria, Yemen, Iran da sauran sassan yankin.
Ya ce ya kamata a duba abubuwan da ke faruwa bisa halin da ake ciki a zahiri, yana mai cewa ba za a iya tabbatar da duk wani mataki da sunan yaƙi da ta’addanci ba.
Ya tambayi masu kai hare-hare kan fararen hula da wuraren jama’a cewa:
“Shin ɗalibanmu marasa laifi a Minab ’yan ta’adda ne?”
Ya kuma yi tambaya kan ko za a iya bayyana kai hari kan gidaje, asibitoci da sauran wuraren jama’a a matsayin matakan yaƙi da ta’addanci.
Halin da ake ciki a Gaza
Shugaban Iran ya soki hana al’ummar Gaza samun abinci da ruwa tare da kai hare-hare kan mata, yara da tsofaffi.
Ya ce irin waɗannan matakai ba su dace da ikirarin mutunta haƙƙin ɗan Adam ba, yana mai cewa ya kamata al’ummar duniya ta mai da hankali sosai kan lamarin.

Source: Getty Images
Pezeshkian ya kuma zargi Amurka da kasa cika wasu alkawuran da ta ɗauka yayin tattaunawa da kuma yarjejeniyoyi.
Gargadin Amurka game da Iran
A wani labarin, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka mai kula da harkokin Iran ya buƙaci ’yan Amurkan da ke ƙasar su fice nan take ranar Lahadi.
Amurka ta yi magana ne tana mai gargadin yiwuwar soke zirga-zirgar jiragen sama da kuma rufe sararin samaniyar saboda wasu rikice-rikice.
Ofishin ya bayyana yanayin tsaron ƙasar a matsayin mai sarkakiya, tare da yiwuwar samun ƙarin rikici ba zato ba tsammani a Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

