An Sanar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Jihar Yobe, APC Ta Sha Kaye a Mazabu 2
- Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka fafata a zaben ranar Asabar da ta gabata a jihar Yobe
- Hukumar zabe ta YSIEC ta ce an gudanar da zaben cikin nasara a mazabu 178 da ƙananan hukumomi 17 na jihar
- Jam’iyyun adwa na APP da ADP sun samu kujerun kansiloli guda ɗaya kowannensu a Fune da Karasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe, Nigeria - Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka fafata a zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a jihar Yobe.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe (YSIEC) ce ta bayyana sakamakon zaben ranar Lahadi a hedikwatarta da ke Damaturu, babban birnin jihar.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa yayin da yake bayyana sakamakon, shugaban YSIEC, Dakta Ibrahim Mohammed Yabani, ya bayyana cewa an gudanar d zaben ba tare da wata matsala ba.
Jam'iyyu 10 duka fafata a Yobe
Ya kar da cewa an gudanar da zaben cikin nasara a dukkan mazabu 178 da ƙananan hukumomi 17 na jihat Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ibrahim Yabani ya ce jam’iyyun siyasa 10 ne suka shiga zaben, inda suka tsayar da ‘yan takara a kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da kujerun kansiloli a mazabu 178.
Ya ce:
“Wannan damar da aka samu ta shiga zaben na nuna irin yadda aka fafata sosai a zaben a wasu ƙananan hukumomi da dama na jihar.”
APC ta lashe kujerun ciyamomi 17
A cewarsa, bayan gama zabe ranar Asabar, an kirga kuri’u tare da ƙidaya su, inda aka bayyana sakamakon kujerun kansiloli a matakin mazabu, yayin da aka bayyana sakamakon kujerun ciyamomi cibiyoyin tattara sakamako na kowace ƙaramar hukuma.
Sakamakon da hukumar ta bayyana ya nuna cewa APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17.
Duk da nasarar da jam'iyyar APC ta samu na lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi, jam’iyyun adawa biyu sun samu kujerun kansiloli a zaben.
An kayar da APC a mazabun kansiloli 2
Shugaban hukumar YSIEC ya ce jam'iyyar adawa ta APP ta samu kujerar kansila ɗaya a Karamar Hukumar Fune, yayin da jam'iyyar ADPnta samu kujerar kansila ɗaya a Karamar Hukumar Karasuwa.
Ibrahim Yabani ya ce hukumar za ta ci gaba da gudanar da sauran matakan da suka wajaba sakamakon kammala zaben.

Source: Twitter
Bayan kammala zaben, ana sa rana hukumar YSIEC z ata bai wa wadanda suka zamu nasara takardar shaida kafin daga bisani a sa lokacin rantsar da su a hukumance.
APC ta lashe zaben ciyamomi a Enugu
A wani labarin, kun ji cewa jm’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 17 a zaben ƙananan hukumomin Enugu na ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2026.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Enugu (ENSIEC) ce ta bayyana sakamakon zaben bayan kammala tattara sakamakon kuri'un da aka kada a jiya Lahadi.
A cewar shugaban ENSIEC, jam’iyyar APC ta kuma lashe dukkan kujerun kansiloli 260 da ke cikin mazabu 260 na siyasa a fadin jihar Enugu.
Asali: Legit.ng

