2027: Obi da Kwankwaso Sun Ziyarci Sarkin Musulmi a Sokoto

2027: Obi da Kwankwaso Sun Ziyarci Sarkin Musulmi a Sokoto

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun kai ziyara fadar Sarkin Musulmi a Sokoto
  • Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana tare da guje wa kalaman da za su iya haddasa ƙiyayya
  • Ya kuma bukaci ‘yan siyasa su mutunta juna, su kare haɗin kan Najeriya tare da tabbatar da cewa kamfen ɗinsu bai zama sanadin rikici ko rarrabuwar kai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sun kai ziyara fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

Ziyarar ta zo ne yayin da Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan siyasa da su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da guje wa kalaman da za su iya haddasa ƙiyayya da tashin hankali a cikin al’umma gabanin zaɓen 2027.

Rabiu Kwankwaso Sarkin Musulmi da Peter Obi NDC
Sarkin Musulmi a tsakiyar Rabiu Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Sanata Rabiu Kwankwaso ta tabbatar da kai ziyarar tare da wallafa hotuna a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kiran da Sarkin Musulmi ya yi

Sarkin Musulmi ya bukaci a rika siyasa cikin mutunci a lokacin da ya karɓi bakuncin Obi, Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar, Dr Shamsu Haido, a fadarsa da ke Sokoto.

Ya bukaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta juna, su kare haɗin kan ƙasa tare da guje wa zage-zage, cin mutunci da sauran abubuwan da za su iya jawo tashin hankali.

Sarkin ya ce ‘yan siyasa na da damar gabatar da manufofinsu tare da neman goyon bayan masu zaɓe, amma dole ne su yi hakan cikin mutunta doka da kuma mutanen da ke da ra’ayoyin siyasa daban da nasu.

Siyasa ba da gaba ba

Sultan ya jaddada cewa bai kamata a yi amfani da siyasa wajen raba kan al’umma ko haifar da gaba ba, yana mai cewa ya kamata a kiyaye muradun Najeriya da zaman lafiyar ƙasar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana so Tinubu ya hakura da shiga takarar zaben 2027

Sarkin Musulmi ya ce mukaman siyasa na wucin gadi ne, yayin da zaman lafiya da haɗin kai ke da muhimmanci wajen ci gaban al’umma.

Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa, musamman masu neman mukaman gwamnati, da su zama abin koyi tare da tabbatar da cewa kamfen ɗinsu bai zama hanyar haifar da rikici ko rarrabuwar kai ba.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
'Yan takarar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a wajen taro. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Leadership ta wallafa cewwa, a nasa jawabin, Obi ya gode wa Sarkin Musulmi bisa karɓar tawagar da kuma sauraron su. haka zalika shi ma Rabiu Musa Kwankwaso.

Maganar tazarcen Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 domin kammala abin da ya bayyana a matsayin tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Kano yayin bikin ƙaddamar da rabon motoci 50 da Tompolo ya bayar domin tallafa wa gangamin jam’iyyar APC na neman kuri’u gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce Arewa ta kammala wa’adin mulkinta na shekara takwas a ƙarƙashin marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari tsakanin 2015 zuwa 2023, don haka saura Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng