Kotu Ta Sa Rana, za a Saurari Karar Atiku kan Neman Hana Tinubu Takara
- Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC sun nemi Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba su damar gyara ƙarar da suka shigar kan cancantar shigar Shugaba Bola Tinubu takara
- Mai shari’a Inyang Ekwo ya sanya ranar 13 ga Oktoba 2026 domin sauraron buƙatar gyaran ƙarar, bayan tabbatar da cewa an sanar da dukkan waɗanda ƙarar ta shafa
- Ƙarar ta kuma ƙunshi APC da INEC, yayin da ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ake takaddama a kai ya shafi bambancin suna da ake zargin yana cikin takardar NYSC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC sun nemi gyara ƙarar da suka shigar kan cancantar Shugaba Bola Tinubu na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron buƙatar zuwa ranar 13 ga Oktoba 2026. Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 tana gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo.

Source: Facebook
An isar da takardun ƙara
Punch ta wallafa cewa a zaman kotun, lauyan Atiku da ADC, Joseph Silas, ya shaida cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara a cikin wa’adin da kotu ta kayyade.
Ya kuma ce waɗanda suka shigar da ƙarar sun karɓi takardun tare da mayar da martani ga takardun da sauran ɓangarorin suka gabatar.
Sai dai tun farko an samu tsaiko a shari’ar saboda takaddama kan yadda za a isar da takardun ƙarar ga Shugaba Tinubu.
Lauyan Bola Tinubu ya magantu
Lauyan Shugaba Tinubu, Cif Wole Olanipekun, SAN, ya tunatar da kotu cewa a zaman ranar 1 ga Satumba 2026, lauyan INEC, Popoola Owosanya, ya bayar da shawarar karɓar takardun kotun a madadin shugaban ƙasar.
Olanipekun ya ce lauyan masu ƙara ya ƙi karɓar wannan shawara, daga baya kuma ya je kotu domin neman izinin isar da takardun ga Tinubu ta wata hanyar daban.
Ya kuma zargi masu ƙarar da ƙoƙarin yaudarar kotu ta hanyar cewa sun kasa isar da takardun ga shugaban ƙasar. Sai dai Mai Shari’a Ekwo ya bukaci lauyoyin su mayar da hankali kan batun da kotu ke sauraro.
Kotun ta sanya ranar shari'a
Bayan haka, Joseph Silas ya sanar da kotu cewa masu ƙarar sun gabatar da buƙatar gyara takardar ƙarar da suka fara gabatarwa.
Rahoton the Sun ya bayyana cewa ya ce an sanar da lauyoyin waɗanda ake ƙara game da wannan buƙata.
Bayan tabbatar da cewa an isar da buƙatar ga lauyoyin sauran ɓangarorin, Mai Shari’a Ekwo ya ɗage shari’ar zuwa ranar 13 ga Oktoba 2026 domin sauraron buƙatar gyaran ƙarar.
Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ci gaba da neman sababbin basussuka yayin da ’yan Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki.
Atiku ya mayar da martani kan shirin neman sabon bashin dala biliyan1.5 daga Bankin Duniya, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta fara bayyana yadda aka yi amfani da kudin da aka karɓa a baya.
Ya ce iyalai na fama da matsalar samun abinci, man fetur da wutar lantarki, yayin da bashin ƙasar ke ci gaba da ƙaruwa. Atiku ya tambayi yadda aka yi da kudin da aka karbo a baya.
Asali: Legit.ng

