Ko Gezau: Shugaban Iran Ya Sha Alwashi gaban Shugabannin Duniya bayan Barazanar Trump

Ko Gezau: Shugaban Iran Ya Sha Alwashi gaban Shugabannin Duniya bayan Barazanar Trump

  • Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar magana a Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai cewa Iran ba za ta mika wuya ba
  • Pezeshkian ya zargi Amurka da “ta’addanci” kan kisan tsohon Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a farkon yaƙin
  • Ya kuma ce Iran ba za ta bari a yi amfani da mashigar Hormuz wajen kai hari ko ƙarfafa matsin lamba kan ƙasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

New York, Amurka - Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi kakkausar magana a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya ce Iran ba za ta taɓa mika wuya ba.

Wannan shi ne karon farko da Pezeshkian ya yi jawabi a Majalisar Ɗinkin Duniya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran.

Pezeshkian ya soki Trump
Masoud Pezeshkian rike da hoton Ali Khamenei a taron UNGA Hoto: Timothy A. Clary
Source: Getty Images

Tashar BBC ta kawo rahoton cewa Masoud Pezeshkian ya yi jawabin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Shugaban kasa ya je har Amurka ya yi raga raga da Donald Trump

Pezeshkian ya zargi Amurka da ta’addanci Pezeshkian ya zargi Amurka da “ta’addanci” saboda kisan tsohon Jagoran Ƙoli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya mutu a farkon yaƙin.

A yayin jawabin, shugaban Iran ya daga hoton marigayi Khamenei, kafin ya jaddada cewa Iran ba ita ce ta fara yaƙin ba.

Ya ce duk da ƙarin takunkumai da matsin lamba, al’ummar Iran za su ci gaba da nuna adawa.

“Ya kamata Trump ya sani cewa juriyar al’ummar Iran za ta ƙara ƙarfi yayin da ake ƙara takunkumi, matsin lamba da danniya. Ba za mu taɓa sunkuyar da kai ko durƙusawa ba,” in ji Pezeshkian.

Trump ya yi barazanar Iran

Jawabin Pezeshkian ya zo ne kwana guda bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa yana tunanin yiwuwar shafe Iran daha doron kasa.

Sai dai Trump ya kuma yaba wa sababbin tattaunawar da aka sake farawa tsakanin masu shiga tsakani daga Iran da Amurka domin neman hanyar kawo ƙarshen yaƙin da ya tsaya cik.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Donald Trump ya canza sunan fasahar AI

Pezeshkian bai ambaci waɗannan tattaunawa ba a cikin jawabin nasa.

Iran ta yi gargaɗi kan mashigar Hormuz

Pezeshkian ya kuma ce Tehran ba za ta bari a yi amfani da mashigar Hormuz wajen kai wa Iran hari ba, The Guardian ta dauko rahoton.

An samu takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin tun bayan fara yaƙin, lamarin da ya taimaka wajen haifar da tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya.

“Ba za mu bari wasu su samu damar yin amfani da wannan mashigar cikin ’yanci domin ƙarfafa muradunsu ba, yayin da a lokaci guda suke amfani da shi wajen kai mana hari,” in ji shi.

Pezeshkian ya samu damar shiga Amurka

Halartar Pezeshkian a babban taron diflomasiyyar Majalisar Ɗinkin Duniya da ake gudanarwa a Manhattan ta kasance cikin shakku, saboda rashin tabbas kan ko gwamnatin Amurka za ta ba shi takardar izinin shiga ƙasar.

Daga bisani Washington ta ba shi izinin shiga, amma ta ƙi bayar da biza ga wasu daga cikin jami’an da ke cikin tawagarsa.

Kara karanta wannan

Amurka ta gamu da asara da jirgin yakinta ya rikito daga sararin samaniya

Pezeshkian ya yi magana a UNGA
Masoud Pezeshkian na magana a taron UNGA Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Shugaban Brazil ya ragargaji Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya ragargaji shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Lula da Silva ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump, ba shi da ikon mulkin wasu ƙasashe ko tilasta musu bin abin da yake so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng