"Za Su Sha Mamaki"; Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Iya Faruwa da Tinubu a 2027

"Za Su Sha Mamaki"; Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Iya Faruwa da Tinubu a 2027

  • Primate Elijah Ayodele ya yi gargadin cewa Shugaba Bola Tinubu na iya fuskantar matsala a zaɓen 2027 idan bai ɗauki matakan magance rashin gamsuwar jama’a ba
  • Malamin ya ce wasu daga cikin mutanen da ke nuna goyon baya ga gwamnatin Tinubu na iya sauya matsayinsu a lokacin zaɓe
  • Ayodele ya ce kashe kuɗi kaɗai ba zai tabbatar wa jam’iyyar APC nasara ba, yana mai cewa yanayin siyasar 2027 zai bambanta da zaɓukan baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Primate Elijah Ayodele ya yi gargadin cewa Shugaba Bola Tinubu na iya fuskantar matsala a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Primate Ayodele ya ce Tinubu zai fuskanci matsalar ne idan bai ɗauki matakan gaggawa domin magance abin da ya bayyana a matsayin rashin gamsuwar jama’a da gwamnatinsa ba.

Kara karanta wannan

An farmaki magoya bayan Kwankwaso da Peter Obi a wurin gangamin siyasa, bidiyo ya fito

Primate Ayodele ya yi hasashe kan Tinubu
Primate Ayodele na jawabi a coci Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele
Source: Facebook

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, 22 ga Satumba, wadda mai magana da yawunsa, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu.

Ayodele ya ce Tinubu na buƙatar ƙara aiki

A cewar sanarwar da Legit.ng ta samu, malamin ya ce idan aka gudanar da zaɓe a yanzu, abin da zai iya faruwa ba zai kasance mai sauƙi ga Tinubu ba.

Ayodele ya danganta hakan da abin da ya bayyana a matsayin ƙara nuna fushi da rashin jin daɗi tsakanin ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na al’umma.

“Idan aka gudanar da zaɓe a yau, damar Shugaba Tinubu ta samun nasara ba ta da ƙarfi sosai. Ba tabbas ba ne zai lashe zaɓen saboda har yanzu akwai aiki da yawa da ya kamata a yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin masu fada a ji da ke kusa da gwamnati na iya kasancewa ba su gamsu da yadda ake tafiyar da gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

“Mutane suna fushi da wannan gwamnati, har da masu fada a ji. Ko waɗanda ke murmushi tare da shi ba sa jin daɗin gwamnati, kuma za su iya sauya matsayinsu a ƙarshe,” in ji Ayodele.

“Yanayin siyasar 2027 zai bambanta”

Malamin ya ce Shugaba Tinubu na bukatar fahimtar cewa yanayin siyasar ƙasar ya sauya, kuma zaɓen 2027 ba zai kasance kamar zaɓukan baya ba.

Ya jaddada cewa ƙarfin kuɗi kaɗai ba zai wadatar wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar da ke mulki ba.

“Dole Tinubu ya yi aiki tuƙuru idan yana son lashe zaɓe mai zuwa. Ba za a yi komai kamar yadda aka saba ba, kuma bisa abin da nake gani, zai iya fuskantar mamaki idan ba a gaggauta gyara kura-kurai ba,” in ji shi.

Ayodele ya ƙara da cewa wasu ’yan Najeriya na son ganin an sauya gwamnati, sai dai waɗanda ke cikin gwamnati ba sa ganin hakan.

“Mutane suna matuƙar son a sauya wannan gwamnati, amma ba su gani ba tukuna. Mutanen gwamnati suna ganin za su iya sayen hanyar shiga mulki, amma za su sha mamaki,” in ji shi.

Ya ce goyon baya na iya sauyawa

Kara karanta wannan

Shettima ya yi magana da aka fahimci kalamansa a baibai kan Tinubu

Ayodele ya kuma ce rashin gamsuwar da ake zargin tana tsakanin jama’a ba ta tsaya kan ’yan adawa kawai ba.

Ya yi ikirarin cewa wasu mutanen da ke nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu a bainar jama’a na iya kasancewa ba su gamsu da gwamnati a ɓoye ba, kuma za su iya janye goyon bayansu a lokacin da ya fi muhimmanci.

Ya ce zaɓen 2027 ba zai kasance fafatawa kan wanda ya fi kashe kuɗi ba, yana mai gargadin cewa jam’iyyar da ke mulki na iya fuskantar ƙalubale idan ba ta fara ɗaukar matakan da suka dace ba.

Ayodele ya yi hasashe kan Tinubu
Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Qadiriyya ta goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran ƙungiyar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin neman wa’adi na biyu a ofis.

Kungiyar Qadiriyya za ta fara gudanar da addu’o’i ga Shugaba Tinubu, inda za a mai da hankali kan zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng