NLC Ta Bude Kofar Tattaunawa da Gwamnati, Ma'aikata na Iya Samun Karin Albashi
- Kungiyar NLC ta ce za ta dawo teburin tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi, da ake neman a kara daga N70,000
- Kungiyar da sauran masu dafa mata sun bayyana cewa N70,000 da ake biya yanzu bai isa biyan buƙatun yau da kullum na ma’aikata ba
- Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce ƙungiyar ƙwadago za ta nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa aƙalla rabin N1,000,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta sake buɗe tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa.
Ƙungiyar ta dage cewa albashin N70,000 da ake biya a yanzu bai ƙara isa wajen biyan muhimman buƙatun ma’aikatan kasar nan saboda dalilai da dama.

Source: Twitter
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a yayin taron Rights of Workers Summit da aka gudanar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, a ƙarshen mako.
NLC ta sake magana kan albashi
The Guardian ta ruwaito cewa Ajaero, wanda Mataimakin Shugaban NLC, Audu Amba, ya wakilta a taron, ya ce ƙungiyar ƙwadago za ta matsa a kafa mafi ƙarancin albashi na akalla N500,000.
Ya ce:
“Duk abin da bai kai N500,000 ba ba zai iya biyan bukatun ma’aikata ba. Lokaci ya yi da za a sake duba mafi ƙarancin albashin da ake biya a yanzu, kuma nan ba da jimawa ba za mu fara tattaunawa da gwamnati."
Wannan na zuwa ne yayin da wata kungiya a Abuja ta yi kira ga ’yan Najeriya da su goyi bayan buƙatar a sake duba mafi ƙarancin albashi.
Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin cimma matsaya da Gwamnatin Tarayya na iya ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arzikin da jama’a ke ciki.
Albashin N70,000 ya yi kadan - TUC
Da yake magana a taron, Shugaban Kungiyar TUC, Festus Osifo, wanda Sakataren-Gamawa, Nuhu Toro, ya wakilta, ya ce halin tattalin arzikin ƙasar ya yi matuƙar rage ƙarfin sayen ma’aikata.
Ya ce hauhawar farashin abinci, kuɗin sufuri, haya da kuma hauhawar farashin kayayyaki na daga cikin abubuwan da suka sa albashin N70,000 bai wadatar ba.

Source: Twitter
Osifo ya kuma buƙaci masu ɗaukar ma’aikata su bi dokokin ƙwadago ta hanyar tabbatar da biyan ma’aikata albashi mai adalci tare da inganta jin daɗinsu.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana goyon bayansa ga buƙatar ƙarin albashi, yana mai cewa ma’aikatan Najeriya sun cancanci samun ingantaccen yanayin jin daɗi.
Ana son Tinubu ya kara albashi
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun buƙaci a ƙara masu albashi da kashi 400 cikin 100 a kan N70,000 na yanzu wanda ake ganin ya gaza.
Ma'aikatan sun bayyana cewa tsadar rayuwa ta jefa da yawa daga cikin su a mawuyacin hali, ta inda N70,000 ba za ta iya tsinana masu komai ba idan aka kwatanta da tsadar rayuwa da ake fama da ita.
A cikin jerin bukatun da ta gabatar, kungiyar ma'aikata ta nemi gwamnati ta farfaɗo da tattalin arziki, ƙarfafa darajar Naira da inganta makamashi da kuma kara albashin da ake biyan ma'aikata.
Asali: Legit.ng

