Abin Farin Ciki: Tsohon Kyaftin Din Super Eagles Ta Najeriya Ya Karbi Addinin Musulunci

Abin Farin Ciki: Tsohon Kyaftin Din Super Eagles Ta Najeriya Ya Karbi Addinin Musulunci

  • An ruwaito cewa tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya karɓi Musulunci a birnin Doha, Qatar
  • Rahotanni sun yi ikirarin cewa ɗan wasan ya karanta kalmar Shahada domin tabbatar da musuluntar tasa
  • Troost-Ekong mai shekaru 33 na taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahli da ke buga gasar cin kofin kasar Watar watau Qatar Stars League

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Doha, Qatar - Rahotanni sun yi ikirarin cewa tsohon kyaftin din tawagar yan wasan kwwllon Najeriya wstau Super Eagles, William Troost-Ekong, ya karɓi addinin Musulunci.

An ruwwito cewa Ekong ya musulunta ne bayan ya karanta kalmar Shahada a birnin Doha na kasar Qatar, inda yake taka leda a ƙungiyar Al-Ahli mai buga gasar Qatar Stars League.

Ekong.
Tsohon kyaftin din Super Eagles ta Najeriya, Troost-Ekong Hoto: William Troost-Ekong
Source: Getty Images

Jaridar Goal ta ruwaito hakan ranar Laraba, inda ta ce ɗan wasan na Najeriya ya bayyana musuluntar tasa bayan ya karbi kalmar Shahada a lokacin da yake zaune a Doha.

Kara karanta wannan

Dama ga matasa: Za a ɗauki 'yan soshiyal midiya 4000 domin tallata Bola Tinubu

Troost-Ekong ya karbi musulunci

Wani bidiyo da ke nuna Troost-Ekong yana karanta Shahada ya bazu a kafafen sada zumunta, inda malamin addinin Musulunci Dr Muhammad Salah shi ma ya wallafa bidiyon a Facebook, yana mai cewa ɗan wasan ya karɓi Musulunci.

Daga bisani, wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasashen duniya, ciki har da mujallar wasanni ta Morocco Elbotola da jaridar Masar sun ruwaito cewa tsohon kyaftin din Super Eagles ya karbi Shahada.

Troost-Ekong a kungiyar Al-Ahli

Troost-Ekong, mai shekaru 33, a yanzu yana taka leda a Al-Ahli da ke Doha, bayan ya koma ƙungiyar Qatar Stars League a watan Janairu 2026 kan kwantiragin shekara ɗaya da rabi, bayan ya bar ƙungiyar Al-Kholood ta Saudi Arabia.

Ɗan wasan ya yi fice sosai a tawagar Najeriya, inda ya buga wasanni sama da 70 da Super Eagles tare da jagorantar ƙungiyar a manyan gasannin duniya.

Ya kasance cikin manyan ’yan wasan Najeriya da suka kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka ta 2023 da aka gudanar a Côte d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Troost-Ekong.
Tsohon kyaftin din tawagar yan wasan Najeriya, Troost-Ekong Hoto: Williams Troost-Ekong
Source: Facebook

An zabi dan wasan mai tsaron baya a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar bayan ya zura ƙwallaye uku, ciki har da ɗaya a wasan ƙarshe da Najeriya ta yi da mai masaukin baki.

Troost-Ekong ya kuma wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA da kuma wasannin Olympics, inda ya zama ɗaya daga cikin ƙwararrun ’yan bayan Najeriya da suka shafe shekaru goma da suka gabata.

Rahotannin karɓar Musuluncinsa sun zama wani sabon lamari a rayuwarsa yayin da yake ci gaba da buga ƙwallo a Qatar.

Fitaccen jarumin fim ya musulunta

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen jarumin fim din kasar Amurka, Giancarlo Esposito ya karbi addinin Musulunci yayin da ya je aiki Saudiyya.

Bayanan da suka fito daga Saudiyya sun nuna cewa jarumin ya furta kalmar shahada tare da yin sallah a wani masallaci yayin ɗaukar fim.

Matakin da jarumin ya ɗauka ya biyo bayan kyawawan abubuwan da ya gani a lokacin zamansa a Saudiyya da kuma hulɗarsa da Musulmai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262