Abu Ya Girma: Hukumar EFCC Ta Ayyana Neman Abdulrashid Maina Ruwa a Jallo, Ta Fadi Dalili
- EFCC ta ayyana tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho, Abdulrashid Maina, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo
- Maina ya fuskanci tuhume-tuhume 12 da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da ɓoye kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya
- An yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 61 bayan samunsa da laifi kan wasu tuhume-tuhume
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ayyana tsohon shugaban rusasshiyar kwamitin Gyaran Tsarin Fansho, Abdulrashid Maina, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu ranar Laraba.

Source: Twitter
EFCC ta fara neman Maina
A cikin sanarwar jama’a da EFCC ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta ce:
“Ana sanar da jama’a cewa ABDULRASHEED ABDULLAHI MAINA, wanda hotonsa ya bayyana a sama, hukumar EFCC na nemansa ruwa a jallo kan wani zargin karɓar kayayyakin sat
“Maina, mai shekaru 61, ɗan asalin garin Biu ne a Jihar Borno. Duk wanda ke da wani bayani mai amfani game da inda yake ya tuntube mu a ofisoshin EFCC da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Fatakwal ko Abuja.
"Ko kuma a tuntube mu ta lambar waya 08093322644; ko adireshin imel info@efcc.gov.ng, ko ofishin ’yan sanda mafi kusa da sauran hukumomin tsaro.”
Yadda aka gurfanar da Maina a gaban kotu
An gurfanar da Maina tare da ɗansa, Faisal, a ranar 25 ga Oktoba, 2019, kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da ɓoye kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya.
Daga baya, babbar kotun tarayya ta yanke wa Maina hukuncin zaman gidan yari na shekaru 61, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Mai shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya samu Maina da laifi kan zargin satar Naira biliyan 2 da aka ware wa ’yan fansho, inda ya nuna nadama kan yadda wahala ta yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ’yan fanshon.

Source: Twitter
An samu tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho da laifi kan tuhume-tuhume na biyu, shida, tara, uku, bakwai da 10 cikin waɗanda aka shigar a kansa.
Haka kuma, an same shi da laifin ɓoye ainihin sunansa a matsayin wanda ke da damar sanya hannu kan asusun banki da aka buɗe a UBA da Fidelity Bank.
EFCC na binciken malaman addini
A wani labarin, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC ya tabbatar da cewa suna binciken wasu malamai, fastoci da sauran shugabannin addini kan laifuffukan da suka shafi almundanar kuɗi.
Olanipekun Olukoyede ya ce wasu daga cikin waɗanda ake zargi an riga an same su da laifi kuma kotu ta yanke masu hukuncin zaman gidan yari.
Asali: Legit.ng
