Kungiyar Kare Hakkin Musulmi a Najeriya Ta Yi Magana kan Kama Atiku gabanin Zaben 2027
- MURIC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta guji kama tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kan zarge-zargen badakalar kuɗi
- Ƙungiyar ta ce duk wani mataki kan Atiku a wannan lokaci zai iya aika saƙon da bai dace ba ga ’yan Najeriya
- MURIC ta buƙaci gwamnati ta yi taka-tsantsan yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta yi gargaɗi ga Gwamnatin Tarayya kan kama tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bisa zarge-zargen rashin gaskiya a harkokin kuɗi.
Gargaɗin ya biyo bayan wata takarda da aka kai wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), inda aka nemi a sake binciken zarge-zargen da suka shafi Atiku tun lokacin da yake Mataimakin shugaban ƙasa.

Source: Facebook
MURIC ya hango illar kama Atiku
Leadership t ruwaito vewa hakan ya zo ne tare da damuwar da tsohon Sanata Dino Melaye ya bayyana kan yunƙurin gayyata ko kama Atiku, wanda shi dan takarar shugaban kasa na ADC.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, shugavan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce duk wani mataki kan Atiku a wannan lokaci ba zai dace ba kuma zai aika saƙon mara kyau ga jama'a.
"Yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, muna son yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta guji irin wannan mataki. Bai dace ba, haka kuma, yana da alamun rashin bin ƙa’ida tare da ƙarancin fahimtar yanayin da ake ciki,” in ji shi.
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi taka-tsantsan wajen tafiyar da lamarin da ya shafi Atiku, musamman saboda kusancin zaɓen 2027.
MURIC ta ja kunnen gwamnatin Tinubu
MURIC ta kuma yi gargaɗi kan duk wani salon aiki daga gwamnati da zai iya jawo wa Najeriya mummunan kallo a idon ƙasashen duniya.
Sanarwar ta ce:
“A kowane hali, dole ne Gwamnatin Tarayya ta guji nuna wani salon aiki da zai iya sa a ɗauki Najeriya a matsayin ƙasar da ba ta bin ƙa’ida.
"Mun rasa matsayarmu ta fuskar ɗabi’a, abin da ya rage mana shi ne kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya da al’adunta. Sunan Najeriya a idon duniya yana ƙara lalacewa cikin sauri.”

Source: Twitter
Ƙungiyar ta ce yadda ake tafiyar da lamarin dole ne ya kasance bisa tsarin doka, tare da guje wa matakan da za su iya rage amincewar jama’a da cibiyoyin dimokuraɗiyya.
Atiku ya soki Tinubu kan tsadar fetur
Kun ji cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda farashin man fetur ya kai N1,470 kan kowace lita.
Atiku ya ce 'yan Najeriya yanzu suna biyan N1,470 kan kowace lita, duk da cewa farashin danyen mai a kasuwannin duniya bai kai matsayin da ya taba kaiwa a shekarar 2008 ba.
Asali: Legit.ng

