El Rufai na Tsare, Babban Makusancinsa Ya Fice da Jam'iyyar ADC

El Rufai na Tsare, Babban Makusancinsa Ya Fice da Jam'iyyar ADC

  • Tsohon Mataimakin Shugaban ADC na kasa na Arewa maso Yamma, Mallam Ja’afaru Ibrahim Sani, ya sanar da yin murabus daga jam’iyyar nan take
  • Jafaru Sani, wanda ya taɓa neman tikitin takarar gwamnan Kaduna na 2027, ya ce yana cikin waɗanda suka kafa ADC a jihar da yankin Arewa maso Yamma
  • Murabus ɗin nasa ya zo ne gabanin zaɓen 2027, yayin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kaduna da sauran sassan Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Arewa maso Yamma, Mallam Ja’afaru Ibrahim Sani, ya yi murabus daga jam’iyyar.

Jafaru Sani, wanda ya taɓa neman takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2027, ya sanar da murabus ɗin nasa ne a wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban ADC na Anchau Ward da ke ƙaramar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun samu babbar dama a kwamitin yakin neman zaben NDC

Jafaru Sani ya bar ADC
Tsohon jigo a ADC, Malam Jafaru Sani Hoto: Jafaru Sani
Source: Facebook

Mallam Jafaru Sani ya sanya wasikar murabus dinsa daga jam'iyyar ADC a shafinsa na Facebook, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026.

Jafaru Sani ya ce murabus ɗin ya fara aiki nan take

A cikin wasiƙar, Jafaru Sani ya bayyana cewa matakin murabus ɗin nasa ya fara aiki ne nan take. Ya kuma gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ta yi mata hidima a matsayi daban-daban.

Jafaru Sani ya tuna cewa yana cikin waɗanda suka taka rawa wajen kafa jam’iyyar ADC a jihar Kaduna da yankin Arewa maso Yamma.

“Na gode muku bisa damar da kuka ba ni na yi wa jam’iyyar hidima a matsayi daban-daban, a matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar a jihar Kaduna da Arewa maso Yamma,” in ji shi.

An aika kwafin wasiƙar zuwa ga Shugaban ADC na Ƙasa, Shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma da Shugaban jam’iyyar na jihar Kaduna domin sanar da su matakin.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da dan takarar da ya lashe zaben cike gurbi a Kano

Ba a bayyana inda zai koma ba

Murabus ɗin Jafaru Sani ya zo ne gabanin babban zaɓen 2027, a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa da sauya sheƙa tsakanin ’yan siyasa a Kaduna da yankin Arewa maso Yamma.

Sai dai akwai alamun cewa Jafaru Sani na iya komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ko da yake bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a cikin wasiƙar murabus ɗinsa.

Murabus ɗin nasa ya ƙara jawo hankali kan sauye-sauyen siyasa da ake samu a jihar Kaduna yayin da jam’iyyu ke ci gaba da shirye-shiryensu gabanin zaɓen 2027.

Jafaru Sani ya fice daga ADC
Tsohon mamba a ADC, Malam Jafaru Sani Hoto: Jafaru Sani
Source: Facebook

An kai korafin yaron El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin mutanen mazabar tarayya ta Kaduna North sun kai ƙara ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), kan dan majalisarsu.

Masu korafin sun nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kan wani zargin amfani da hodar iblia da ya shafi ɗan majalisar wakilai, Hon. Mohammed Bello El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng