'Yan Bindiga Sun ga Ta Kansu da Suka Sace Daliban Jami'a a Katsina
- Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Dayi-Malumfashi da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta Katsina
- Mutanen da aka ceto sun haɗa da ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma da kuma wani direban motar haya
- Sojoji sun kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton kai hari, lamarin da ya tilasta ’yan bindigar tserewa tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma (OPFY) sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Dayi-Malumfashi da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Mutanen da aka ceto daga hannun hatsabiban 'yan bindigan sun haɗa da ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da kuma wani direban motar haya.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma ta OPFY, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
A cikin sanarwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja ya ce an ceto mutanen ne a yammacin ranar Litinin, 21 ga Satumba 2026.
Sojoji sun kai ɗaukin gaggawa
Laftanar Kanal Aliyu Danja ya ce sojojin sun samu kiran neman agaji bayan ’yan bindiga sun kai hari kan wata motar haya da ke tafiya daga Kaduna zuwa Katsina.
Ya bayyana cewa sojojin sun gaggauta mayar da martani, lamarin da ya tilasta ’yan bindigar barin waɗanda suka yi garkuwa da su tare da tserewa daga wurin.
Mai magana da yawun rundunar ta Operation Fansan Yamma ya ce duka mutanen bakwai an same su cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani rauni ba.
Hakazalika, ya ƙara da cewa an gudanar da binciken farko kan tsaron su tare da yi musu gwaje-gwajen lafiya kafin a ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace.
An miƙa waɗanda aka ceto ga jami’ai
Daga bisani, an miƙa mutanen da aka ceto ga jami’an da aka ware domin taimaka musu komawa wajen iyalansu da kuma hukumomin makarantarsu, jaridar The Punch ta kawo rahoton.
Rundunar ta Operation Fansan Yamma na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin domin dakile hare-haren ’yan bindiga da sauran ayyukan masu aikata laifuka.

Source: Original
Sojoji sun cafke kwamandojin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar Operation Fansan Yamam tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wasu manyan kwamandojin wata ƙungiyar ’yan ta’adda a Katsina.
Kungiyar 'yan ta'addan ana alakanta da sacewa da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya a Jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani babban kwamanda mai suna Samagi, wanda aka bayyana a matsayin muhimmin jigo a tsarin gudanar da ayyukan ƙungiyar.
Asali: Legit.ng

