Gwamnoni, Ministoci, Malamai, Sarakuna za Su Hadu don Yi wa Najeriya Addu'a

Gwamnoni, Ministoci, Malamai, Sarakuna za Su Hadu don Yi wa Najeriya Addu'a

  • Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta shirya gudanar da addu’ar ƙasa ta musamman domin neman zaman lafiya da tsaro
  • Za a gudanar da addu’ar a Abuja ranar 30 ga Satumba, inda sarakunan gargajiya, gwamnoni da shugabannin siyasa za su halarta
  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ne zai jagoranci addu’ar da za a yi a Masallacin Ƙasa na birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta sanar da shirya addu’ar ƙasa ta musamman domin neman taimakon Allah ga Najeriya.

Za a gudanar da taron ne a harabar Masallacin Ƙasa da ke Abuja ranar 30 ga Satumba, daga ƙarfe 4:30 na yamma zuwa 6:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Magana ta yi nisa, 'Tinubu Must Go' ta raba wasikun hada kan Atiku, Obi da sauransu

Masallacin Abuja masallaci
Masallacin kasa da ke Abuja, Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sarakuna, 'yan siyasa za su halarta

Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin waɗanda ake sa ran za su halarci addu’ar akwai gwamnoni, ’yan Majalisar Ƙasa, ministoci da sauran jami’an gwamnati.

Haka kuma ana sa ran halartar sarakunan gargajiya, wakilan ƙungiyoyin Musulunci da Majalisun Harkokin Addinin Musulunci na jihohi.

Sultan na Sokoto kuma Shugaban Majalisar NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ne zai jagoranci addu’ar.

Abubuwan da za a roka

The Cable ta wallafa cewa jami’in Hulɗa da Jama’a na NSCIA, Abbas Jimoh, ya bayyana shirin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce taron zai kasance wata dama ga Musulmi su haɗa kai wajen neman taimakon Allah ga ƙasar.

Daga cikin batutuwan da za a mayar da hankali a kansu akwai zaman lafiya, tsaro, haɗin kan ƙasa, shugabanci nagari da ci gaban Najeriya.

NSCIA ta buƙaci waɗanda aka gayyata da kuma Musulmi daga sassan ƙasar su yi shirin halartar addu’ar.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira

Taron NSCIA a 1 ga Oktoba

Addu’ar ƙasa za ta kasance gabanin Babban Taron NSCIA da aka shirya gudanarwa a harabar Masallacin Ƙasa na Abuja ranar 1 ga Oktoba.

Taron zai haɗa manyan shugabannin Musulmi da suka haɗa da Sultan, Mataimakin Shugaban Majalisar na Arewa kuma Shehun Borno, Alhaji Abubakar ibn Umar Garbai El-Kanemi.

Haka kuma za a samu Mataimakin Shugaban Majalisar na Kudu, Alhaji Rasaki Oladejo, da Babban Sakatare, Farfesa Is-haq Oloyede, da Mataimakin Babban Sakatare, Farfesa Salisu Shehu.

Sarkin Musulmi a Najeriya
Mai alfarma Sarkin Musulmi na jawabi. Hoto: JNI
Source: Facebook

Za a kuma samu wakilan jihohi 36 da Abuja, gwamnonin Musulmi, ’yan majalisa, ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin Musulunci.

Majalisar ta ce Babban Taron zai kasance wata dama ta yin shawarwari da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi NSCIA, al’ummar Musulmi da kuma Najeriya.

Tawagar Tinubu ta hadu da malamai

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Abdul’Aziz Yari ya ce sun fara shirin kamfen ɗin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu ta hanyar ganawa da ’yan Najeriya da shugabannin addini.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun samu babbar dama a kwamitin yakin neman zaben NDC

Yari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci Kano domin ganawa da shugaban ƙungiyar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, inda ya ce sun fi bai wa sauraron ’yan Najeriya kai tsaye muhimmanci.

Ya ce tawagar ta ziyarci Bauchi, Jos da Kaduna, inda ta gana da shugabannin Izala da Tijjaniyya, kafin ta je Kano domin neman addu’a da jagorancin malamai na ƙungiyar Qadiriyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng