Da Gaske Sarki Sanusi II Ya Fadi Jarabawa da Ya Koma Karatu Jami'a a Kano?
- Majalisar Masarautar Kano ta musanta wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu carry-over
- Masarautar ta ce Sarkin Kano, wanda ke karatun digiri na LL.B a fannin Shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano, yana kan hanyar kammala karatunsa da darajar First Class
- Sakataren Ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ya bayyana cewa bisa bayanan da ke hannun masarautar, maki guda ne kacal ya rage wa Sarkin domin samun daraja mafi girma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Majalisar Masarautar Kano ta yi watsi da wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya samu carry-over a daya daga cikin darussan karatunsa na Shari’a.

Kara karanta wannan
Saƙon da Bola Tinubu ya tura wa 'yan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya da wasu ƙasashe
Bidiyon, wanda ya yadu sosai a kafafen sada zumunta ranar Lahadi, ya nuna kamar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) bai cika sharudan karatu a daya daga cikin darussansa ba.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa Sarki Sanusi yana shekara ta 2 na karatun digiri a fannin lauya da Shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano.
Matsayin Sarki Sanusi a jami'a
Sakataren Ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ya ce zargin da bidiyon ya kunsa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa sarkin yana kan hanyar kammala karatunsa da matakin First Class.
Ado ya ce bayanan da ke hannun Masarautar Kano sun nuna cewa maki guda ne kacal ya rage wa Sarkin domin samun matakin First Class.
Ya ce an dauki bidiyon ne a wani shiri da daliban Shari’a na jami’ar suka shirya ranar Asabar:
“Mun halarci wani shiri da daliban Shari’a na jami’ar suka shirya ranar Asabar, kuma wani dalibi ne ya dauki bidiyon. Amma ba gaskiya ba ne.
“A lissafinmu, maki guda ne kacal ya rage wa Sarkin ya samu darajar First Class”

Source: Twitter
An musanta faduwar Sarki jarabawa

Kara karanta wannan
"Jarumar fina finan Najeriya ta mutu a ofishin ƴan sanda," Saurayinta ya yi zargi
Wani dalibin jami’ar, Ibrahim Abubakar-Danmasani, shi ma ya yi watsi da ikirarin, yana mai cewa har zuwa ranar Lahadi ba a fara jarabawar jami’ar ba.
A bayanin da dalibin ya yi, ya ce ana sa ran fara jarabawar ne ranar Litinin.
Majiyoyi daga cikin jami’ar sun kuma tabbatar da matsayin Masarautar Kano, inda suka ce bidiyon da ya yadu bai nuna ainihin halin karatun Sarkin ba.
Majiyoyin sun danganta bidiyon da wasu matasa da ake zargin sun dauke shi tare da yada shi a matsayin wasa.
Abba ya yaba wa sarakuna
A wani labarin, mun ruwaito cewa Abba Kabir Yusuf, ya yabawa sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci da gwamnonin Arewa maso Yamma bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar shirin auren gata na jihar.
Gwamnan ya yi godiya ta musamman ga Shugaban Majalisar Sarakunan Kano da Sarakunan Kano, Rano, Karaye da Gaya bisa jagoranci, addu’o’i da gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da taron.
Haka kuma, ya yaba wa malaman da suka zo daga sassa daban-daban na ƙasar domin halartar taron, tare da bayyana addu’o’insu da shawarwarinsu a matsayin muhimmin ginshiki wajen nasarar shirin.
Asali: Legit.ng