Kasar Saudiyya Ta Bullo da Wani Tsari, Kudin Kujerar Hajji Zai Kara Tsada a Najeriya

Kasar Saudiyya Ta Bullo da Wani Tsari, Kudin Kujerar Hajji Zai Kara Tsada a Najeriya

  • Hukumar NAHCON ta ce kuɗinn kujerar aikin Hajji na iya ƙaruwa saboda sababbin manufofin da kasar Saudiyya ta ƙirƙiro
  • Kuɗin Hajjin 2027 a yanzu yana tsakanin N7.5m zuwa N7.8m, gwargwadon wurin da mahajjaci ya fito a Najeriya
  • Saudiyya na shirin soke tsarin Grade D da mahajjatan Najeriya suka dogara da shi wajen samun rangwame kuɗin Hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa kuɗin kujerar Hajji na iya ƙaruwa sakamakon sababbin manufofin da Masarautar Saudiyya ta ƙirƙiro.

Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Yusuf, ne ya bayyana yayin wani taron manema labarai ranar Litinin, ina ya ce kudin hajjin zai sauya ne cikin shekaru uku masu zuwa.

Hajji.
Wasu mahajjatan Najeriya mata yayin da suke shirye-shiryen dawowa gida bayan kammala aikin Hajji a Saudiyya Hoto: NAHCON
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kuɗin Hajjin 2027 yana tsakanin N7.5m zuwa N7.8m, gwargwadon wurin da mahajjaci ya fito a Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Wike ya yi damara, zai gwabza da shugaban gwamnonin APC

Dalilin da zai jawo karin kudin Hajji

Ambasada Yusuf ya ce za a samu karin ne saboda hukumomin Saudiyya na shirin soke tsarin hidimar Grade D da mahajjatan Najeriya suka dogara da shi wajen rage kuɗin kujerar Hajji.

Ya ce soke tsarin na daga cikin sauye-sauyen da za su mayar da harkokin Hajji a hannun ƙwararru, tare da rage kaso da gwamnati ke kula da shi zuwa 2%, yayin da kamfanonin yawon bude ido za su kula da kashi 98 na mahajjata.

Ya ce an dage aiwatar da sauyin da aka shirya fara yi a bana zuwa shekaru uku masu zuwa sakamakon ƙoƙarin diflomasiyya da hukumar NAHCON ta yi.

Talakawa sun fi amfana da Grade D

Shigaban NAHCON ya ce:

“Idan ka fahimci yanayin mahajjatan Najeriya, za ka san cewa 80 zuwa 90% na mahajjata talakawa ne waɗanda saboda kishinsu ga addininsu suke tara kuɗi a hankali na tsawon lokaci domin su samu damar sauke wannan farilla. Saboda haka, mafi yawansu suna cikin tsarin Grade D.

Kara karanta wannan

Yadda mutanen Tinubu suka zagaya kan malaman Izala da Darika a Najeriya

“Yayin da muke ci gaba, gwamnatin Saudiyya za ta soke tsarin Grade D saboda sun yi imanin cewa duk wanda ya zo gudanar da Hajji ya kamata ya samu kyakkyawar kwarewa.
“Suna shirin samar da horar da ma’aikata a matakai daban-daban, ta yadda duk wanda zai kula da harkokin Hajji ya kasance ƙwararre. Kma suna sa ran cewa sai mutum ya samu takardar shaidar wannan horo kafin a amince da shi a matsayin mai kula da harkokin Hajji,” in ji shi.
Shugaban NAHCON.
Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON), Ambasada Isma'il Yusuf Hoto: Hajji Kiran Allah
Source: Facebook

Sai dai Ambasada Yusuf ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa hukumar za ta ci gaba da taka rawar da ya dace domin tabbatar da cewa ba a yi watsi da jin daɗin mahajjata ba.

Saudiyya ta ki amincewa da bukatar NAHCON

Kun ji cewa hukumar NAHCON ta sanar da cewa Masarautar Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar Najeriya ta ƙara yawan guraben da aka ware wa ƙasar domin aikin Hajjin 2027.

Tun farko dai, Najeriya za ta samu gurbi 50,000, wanda ya haɗa da 35,000 na mahajjatan da suka fito daga bangaren gwamnati da 15,000 na kamfanonin yawon buɗe ido

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262