Sauki Ya Samu: Dangote da 'Yan Kasuwa Sun Sauke Farashin Man Fetur

Sauki Ya Samu: Dangote da 'Yan Kasuwa Sun Sauke Farashin Man Fetur

  • Matatar Dangote da wasu dillalan man fetur sun rage farashin fetur a manyan ma’ajiyoyi da ke Lagos, Fatakwal, Calabar da Warri
  • Rahoton farashin man fetur na baya-bayan nan ya nuna cewa wasu kamfanoni sun rage farashin litar fetur da tsakanin N20 zuwa N25
  • Wannan saukar farashin ya zo ne yayin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya ragu, lamarin da ya samar da damar rage farashin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Matatar Dangote da sauran dillalan man fetur sun rage farashin man fetur a wasu manyan ma’ajiyoyi a Najeriya, yayin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ke raguwa.

Hakan na zuwa ne yayin da Aliko Dangote ya ba jama'a damar sayen hannun jarin matatar shi da ke Legas.

Kara karanta wannan

Ana hurawa Tinubu wuta ya rage kudin litar man fetur zuwa N500

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton farashin ma’ajiyar man fetur na baya-bayan nan da Petroleumprice.ng ta wallafa ya nuna cewa sauye-sauyen farashin sun fi yawa a Lagos.

Matatar Dangote ta rage farashi

Punch ta wallafa cewa a Lagos, matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,350 zuwa N1,325, wanda ke nufin an rage N25 kan kowace lita.

Kamfanonin Ascon, Integrated, Pinnacle da Sahara su ma sun rage farashin da N24, inda litar fetur dinsu ke tsakanin N1,326 zuwa N1,327.

Kamfanin MRS ya rage farashinsa da N20 zuwa N1,332 kan kowace lita, yayin da Wosbab ke sayar da litar a N1,330.

Rage farashin ya zo ne yayin da farashin danyen mai na Brent ya fadi kasa da dala 100 kan ganga, yayin da WTI, ma’aunin farashin mai na Amurka, ya koma dala 91.17 kan ganga.

Fetur ya sauka a wasu jihohi

A Fatakwal, Masters ya rage farashin fetur da N2 zuwa N1,328 kan kowace lita, yayin da Stockgap ya rage N7 zuwa N1,323.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanar da karyewar farashin sufuri a Najeriya, ya kafa hujja da Kaduna da wasu jihohi

Kamfanonin Bulk Strategic da Sigmund sun sanya farashin fetur a N1,328, yayin da Matrix ya ci gaba da sayar da shi a N1,330.

A Calabar, Mainland ya samu mafi karancin farashin fetur cikin wuraren da rahoton ya kunsa, bayan da ya rage farashin da N7 zuwa N1,320.

Alkanes ya rage farashinsa da N2 zuwa N1,325, yayin da Matrix ya ci gaba da N1,330. Sobaz kuwa ya kara N1, inda ya koma N1,328.

Gidan mai a Najeriya
Ana sayar da fetur a gidan man Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A Warri ma an samu sauye-sauye daban-daban, ko da yake mafi yawan canje-canjen sun kasance na rage farashi.

Keonamex ya rage farashin litar fetur da N3 zuwa N1,327, yayin da Nepal da Prudent suka rage N1 da N2, inda farashinsu ya koma N1,329 da N1,328.

Matrix da Optima kuwa sun kara farashin fetur da N3 da N1, inda suka koma N,330 da N1,328.

Farashin dizal ma ya ragu

A kasuwar man dizal, wanda aka fi sani da AGO, an kuma samu raguwar farashi a wasu wurare.

A Lagos, Chipet ya rage farashin dizal da N15 zuwa N1,815 kan kowace lita, yayin da Ascon, Duport da Integrated suka rage N5, inda suka koma farashi iri daya.

Kara karanta wannan

An dakatar da babban jami'in tsaro kan mutuwar kusan mutum 40

Ibachem, Ibeto, Dangote, Obat da Pinnacle sun sayar da dizal a farashin da ke tsakanin N1,815 da N1,860.

A Fatakwal, Masters ya rage farashin dizal da N35 zuwa N1,900 kan kowace lita.

Dangote ya shiga harkar wuta

A wani labarin, kun ji cewa hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote ya ce kamfaninsa na shirin zuba sama da dala biliyan 10 a bangaren samar da wutar lantarki.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce rashin daidaiton manufofin gwamnati da karancin wutar lantarki na daga cikin matsalolin da ke hana ‘yan Afirka zuba jari a nahiyar.

Ya ce kamfaninsa na duba yiwuwar karkatar da kudin da aka ware wa wasu harkokin kasuwanci, ciki har da karafa, zuwa samar da wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng