Atiku Ya Jero Mutane 3 da Ya Kamata Su Amsa Tambayoyi kan Mutuwar Matasa 37 a Hannun NSCDC

Atiku Ya Jero Mutane 3 da Ya Kamata Su Amsa Tambayoyi kan Mutuwar Matasa 37 a Hannun NSCDC

  • Tsohon mataimakin s ohhugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar mutane 37 a hannun NSCDC
  • Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa guda biyu na da tambayoyin da ya kamata su amsa kan lamarin
  • Gwamnatin Tarayya ta riga ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wadanda aka tsare a Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya jero mutane uku da ya kamata su amsa tambayoyi kan yadda matasa 37 suka mutu a hannun NSCDC a Neja.

Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu, Ministan Ma’adinai na Kasa, Dele Alake, da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, su ya kamata dora wa laifin mutuwar matasan a kansu.

Kara karanta wannan

An saki sunayen jami'an NSCDC 20 da aka dakatar kan mutuwar mutum 37 a Neja

Atiku Abubakar.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A rahoton The Cable, iAtiku ya ce bai kamata a bar mutuwar ‘yan Najeriya 37 da aka kama bisa zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Neja ta wuce ba tare da bankado gaskiya ba.

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, Atiku, ya ce jami’an gwamnati sun kama matasan nan raye, suka tsare su, amma ba su mayar da su ga iyalansu a raye ba.

Ya ce:

“‘Yan Najeriya 37, da dama daga cikinsu matasa ne, sun shiga hannun gwamnati a raye, dukansu sun mutu a can."
"Ba Boko Haram ko ‘yan bindiga ne suka kashe su ba. Ba su mutu a fagen daga ba. Sun mutu ne bayan jami’an gwamnatin Najeriya sun kama su, sun kulle su a ofishinsu.
“Gwamnati ta kwace ‘yancinsu kuma ta dauki alhakin lafiyarsu. Yanzu dole ne ta yi bayani kan kowane rai da aka rasa. Ba zai yiwu Tinubu, Dele Alake da Olubunmi Tunji-Ojo su fake da farfaganda ba yayin da iyalai 37 ke binne ‘ya’yansu.”

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta barke kan Atiku ya kira Tinubu da sunan da 'bai dace ba'

Atiku ya kwatanta lamarin da 2014

Atiku ya kwatanta lamarin da ibtila'in da ya garu yayinndaukar ma’aikatan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) na 2014 a filin wasa na kasa da ke Abuja, lokacin da akalla mutane 16 suka mutu.

Ya ce Abba Moro, wanda a lokacin shi ne ministan da ke kula da bangaren, an gudanar da bincike a kansa sannan daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu kan lamarin.

Ya tambayi dalilin da ya sa bai kamata a yi amfani da irin wannan ma’auni da mataki a wannan karon ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Atiku ya zargi Tinubu da ministoci 2

“An kama wadannan ‘yan Najeriya ne a wani samame kan zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, sannan Hukumar NSCDC, wadda Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ke kula da ita, ta tsare su.
“Wadanda suka tsira sun yi zargin cewa an cunkusa su a cikin wani daki mai cike da mutane da rashin isasshen iska, inda suka yi fama da matsalar numfashi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kare kansa daga sabon zargin da APC ta masa da neman hakura da takara

“Wannan zargi na bukatar a gudanar da bincike nan take kuma mai zaman kansa. Ba za a iya warware shi ta hanyar binciken cikin gida ba, inda jami’an gwamnati ke binciken jami’an gwamnati tare da gabatar wa ‘yan Najeriya sakamakon da gwamnati ta amince da shi.”

- Atiku Abubakar.

Tunji Ojo.
Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji Ojo da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Atiku ya ce ya kamata Tunji-Ojo ya yi bayani kan abin da ya faru saboda shi ne ke kula da hukumar da ake zargin mutuwar mutanen ta faru a hannunta.

Ya kuma soki Alake kan ayyukan tabbatar da bin doka a bangaren hakar ma’adinai, yana mai cewa Shugaba Tinubu ne ke da babban alhakin abin da gwamnatinsa ke aikatawa.

Sunayen matasan da suka mutu

Kun ji cewa an bayyana sunayen matasa 37 da suka rasa rayukansu a dakin ajiyar masu laifi na hukumar tsaro ta NSCDC da ke jihar Neja.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta dauki matakin bincike don gano abin da ya faru wanda ya kai ga mutuwar matasa fiye da 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262